Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Kannywood

    Dalilai Uku Ne Suka Sa Na Shigo HarKar Fim – Jaruma Fati Shu’uma

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiSeptember 1, 2022No Comments2 Mins Read

    Kamar yadda muka saba kawo muku labaran Kannywood da dumi duminsu, a wannan karon ma mun kawo muku labarin jarumar Fati Shu’uma.

    Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood mai suna Fatima Abubakar wadda aka fi sani da Fati Shu’uma ta fito fili ta bayyanawa duniya dalilan da ya sa ta shiga harkar fim.

    Jarumar ta bayyana dalilan na ta ne a lokacin da ake fira da ita a gidan talabijin din nan na Hausa na Arewa24 a cikin shirin Ga Fili Ga Mai Doki na Kundin Kannywood tare mashiryin shirin Jarumi Aminu Shariff.

    Amihad.com ta samu cewa jarumar dai ta bayyana cewa tun kafin ta shiga harkar ta ji ana cewa ana iskanci ne a masana’antar wanda a cewar ta wannan ne ma dalili na farko da ya kara cusa mata ra’ayin ta shiga cikin sana’ar domin ta ganewa idanun ta ko hakan gaskiya ne ko a’a.

    Sauran dalilan da jarumar ta zayyana sun hada da samun kudaden kashewa da kuma yin suna da daukaka kamar dai dukkan sauran jarumai

    Da aka tamabaye ta ko fim nawa ta fito a ciki sai jarumar ta ce duk da dai suna yawan gaske don har ma ta nema kirgawa amma dai tana kiyasin cewa sun kai 70.

    Haka zalika jarumar ta bayyana jarumi Adam A. Zango da Jamila Nagudu a matsayin jaruman da suka fi burge ta tun kafin ma ta soma harkar fim din.

    Related Posts

    Shin Dagaske Ne Jaruma Fati Washa Tafi Duk Matan Kannywood Kyau?

    November 24, 2022

    Jaruman Kannywood Sun Jawowa Kansu Magana Saboda Wannan Bidiyo Da Sukayi

    November 20, 2022

    Kalli Bidiyon Maryam Yahaya Tana Rawar Yan Kauye Kafin Ta Shiga Harkar Fim

    November 18, 2022

    Junaidiyya Gidan Badamasi Ta Bayyana Dalilin Dayasa Ta Fito Daga Gidan Mijinta Ta Fara Harkar Fim

    November 18, 2022

    Jerin Matan Da Adam A Zango Yayi Soyayya Dasu A Kannywood

    November 18, 2022

    Kalli Abinda Hamisu Breaker Da Momee Gombe Sukayi A Gidan Gala Wanda Ya Jawo Musu Magana

    November 16, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.