Shahararren ɗan wasan barkwancin nan na masana’antar Kannywood Musa Abdullahi wanda aka fi sani da Musa mai sana’a ya bayyana dalilin da ya sa shi yawan yin nasiha ga ‘yan matan Fim.
A zantawarshi da sashin hausa na gidan Rediyon Amurka ya bayyana cewar dukkanin kalamansa yana yin su ne bisa kishi da kuma inganta sana’ar su ta wasan kwaikwayo.
Wani faifan bidiyo da ya karade kafar sada zumunta ya nuna Musa Mai Sana’a na yi wa wasu mata ‘yan Hausa fim nasiha da gargadi akan yadda ya kamata su taka a sannu a harkar domin makomar rayuwarsu.
Jarumi musa mai sana’a yayi hira da murya amurika voahausa kenan indansuke masa tambaya akan videon da yake baiwa yan matan kannywood shawara akan shiga harka fim.
Bidiyon yayi yawo shafukan sada zumunta inda ake ganin kamar yana dabawa yan fim mata wuka a ciki jarumin yace wannan duk cikin shirinsa mai suna kunnen kashi.
Kuma ya bayyana ita sana’ar mutum kullum so ake ya tsaftace ba domin kuwa anaso ka baiwa addininka hidima wanda ko bayan ranka za’a iya tunawa da kai.
Acewarsa shi ya bada shawara ne saboda mutane su amfa Don Allah bawai dan cin zarafin wani ba.
Yayi bayyanin sosai wanda yace shi ko kadan baiga illar abunda ya fada ba.