Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Family & Relationships

    Duk Namijin Dake Son Zaman Lafiya Kada Ya Fadawa Mace Wadannan Abubuwa Biyar

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiSeptember 1, 2022No Comments3 Mins Read

    A wanii bincike da amihad.com ta gabatar ta kado wasu muhimman abubuwa guda biyar wanda bai kamata a fadawa mata ba saboda wannan kalamai suna fusata mata matuka.

    Saboda haka a matsayin ka namiji ka yi taka tsantsan a lokacin da ka ke hira da mace. A haka ne muke baku da shawara da ku kiya domin wadannan abubuwa wan tattarosu ne bisa ra’ayoyinn mutane.

    Duk da cewa ba wani bincike aka yi a hukumance ba, akwai wasu ka’idoji da ya kamata a kiyayye idan ana magana da mace. Kuma wadannan ka’idoji mutane da dama sun amince dasu.

    Kada ka bari komai ya wuce ka ga tambayoyi biyar da bai kamata namiji ya rika yi wa mata ba, kamar yadda rahoton Premium Times ya tabbatar.

    1. Yaushe za ki yi aure?

    Yan uwa maza, ba huruminka bane ka tambayi takwararka ko abokiyar aikina lokacin da za ta yi aure.

    Mata na samun matsin lamba sosai daga al’umma da iyayensu da dangi kan aure, yi musu wannan tambayar na kara jefa su cikin damuwa. Idan ya zama dole ka yi tambayar, ka tabbatar ka yi cikin yanayin da ya dace na mutuntaka da raha.

    2. Kina kara kiba

    Yin tsokaci kan kibar mace batu ne da ya kamata ka kame bakinka daga furtawa don muna zamani wanda ake danganta kyau yanayin jikin mace.

    Don haka, fada wa mace cewa ta yi kiba ‘tamkar fada mata cewa bata cikin wadanda ake yi wa kallon suna da kyau.

    Hakan na iya shafar kimarta a matsayin mace, ta rika ganin tamkar bata cika ‘ya mace ba. Don haka, duk yadda mace ta ke, ko mai kiba, ko siririya, ka guje yin magana kan jikinta.

    A yi wani hiran daban. Idan kuma ita ta taso da batun, ka san yadda za ka yi dabara ka isar da sakonka cikin hikima.

    3. Shekarun ki nawa?

    Idan dai kai ba likita bane ko jami’in yin rajista, ka guji yi wa mace wannan tambayar, musamman idan haduwarku ta farko ne. Mata da dama ba su son a san shekarunsu, don haka yin wannan tambayar bai cika yi musu dadi ba.

    4. Ba ki da hankali

    Babu wanda ke son a kira shi mara hankali, don haka ka guji kiran matarka ko budurwa ko abikayar aiki mara hankali musamman kokacin da aka samu sabani.

    Idan abu ya shiga tsakanin ka da mace kuma ka na ganin tana kambama abin fiye da kima ka daure ka kwantar da zuciyarka kada ka fada mata bakar magana, don wasu na da riko a zuci sosai.

    5. Kina da juna biyu ne?

    Ina rokon ka a matsayin saurayi dan Najeriya ka guji yin wannan tambayar da mata, idan ba matar ka bane. Tambaya ce wanda ba ta yi wa mata dadi kuma ba hurumin ka bane.

    Wadannan sune abubuwa guda biyar da bincikenmu ya kawo muku, saboda haka sai a kiyaye don neman zaman lafiya.

    Related Posts

    Yadda Kanin Miji Ya Dirkawa Amaryar Yayansa Ciki A Nasarawa

    November 19, 2022

    Sati Biyu Kacal Da Yin Aure Amarya Ta Bukaci Ango Ya Saketa Saboda Baya Iya Gamsar Da Ita A Kan Gado

    November 18, 2022

    Yadda Ake Kwalliyar Maida Tsohuwa Yarinya

    November 7, 2022

    Lokuta Da Yawa Maza Yan Iska Sunfi Iya Soyayya Wata Budurwa Ta Kira Ruwa

    November 5, 2022

    Yadda Ango Yayi Dawowar Bazata Ya Kama Matarsa Da Babban Abokinsa Suna Cin Amanarsa

    November 4, 2022

    Bidiyon Hira Da Matar Da Take Auren Maza Biyu Kuma Suke Kwana Kan Gado Daya

    November 3, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.