An cafke wani magidanci kan zargin yi wa agolarsa mai shekara 15 fyade har ta dauki ciki.
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Ekiti, DSP Sunday Abutu, ya tabbatar da damke magidancin ta wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Ado-Ekiti, babban birnin jihar.
Abutu ya ce bincikensu ya gano yarinyar tana dauke da juna-biyu na wata hudu, kuma ta fada wa ’yan sanda cewa wanda ya yi mata cikin mijin mahaifiyarta ne.
”An damke wanda ake zargin ne a yankin Omuo-Ekiti cikin Karamar Hukumar Ekiti ta Gabas a jihar.
“Yarinyar ta ce uban nata ya soma yi mata fyade ne tun bayan da mahaifiyarta ta haihu inda ta shafe makonni uku a asibiti.
[ads1]
“Yakan yaudare ta zuwa gona sannan ya yi lalata da ita kuma ya yi mata barazanar zai cutar da ita idan ta kuskura ta fada wa wani abin da ya faru a tsakaninsu,” in ji Abutu.
Dan sandan ya ce, magidancin ya ce sharrin shaidan ne ya kai shi ga aikata haka.
Ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu yadda ya kamata.