• Fri. Mar 29th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Duniya Ina Zaki Damu: An Rufe Wata Makaranta Saboda Dalibai Mata Sun Saka Hijabi

ByLucky Murakami

Aug 27, 2022

Mun samu rahoton makarantar da aka kulle saboda dalibai sun saka hijabi wanda abun ya bawa mutane mamaki matuka.

Kamar yadda shugaban makarantar, Phebean Olowe, ya bayyana, an rufe makarantar ne saboda rashin amincewa dalibai mata musulmi su saka hijabi zuwa makaranta.

Makarantar sekandare ta University of Ibadan International School dake garin Ibadan nan jihar Oyo ta rufe makaranta saboda wasu dalibai sun saka Hijabi.

Kamar yadda shugaban makarantar, Phebean Olowe, ya bayyana, an rufe makarantar ne saboda rashin amincewa dalibai mata musulmai na su saka hijabi zuwa makaranta.

A cikin wata wasika da suka tura ma mahukuntan makarantar a ranar 9 ga watan Nuwamba, iyayen yara karkashin kungiyar iyayen dalibai na makarantar (PTA) sun sanar cewa yaran su zasu fara saka hijabi zuwa makarantar.

Kungiyar tayi ikirari cewa bayan ga ibada yara mata na da damar saka hijabi bisa ga yadda dokar kasa ta tanadar.
Sai shugaban majalisar koli na makaranatar

Farfesa Abideen Aderinto ya soki matakin da kungiyar ta dauka.

Yace makarantar ba ta gwamnati bace don haka suna da damar kafa dokoki matukar iyayen makaranta sun amince da shi.

“Duk wanda ke son canja wata doka a makarantar sai ya bi ta hanyoyin da suka dace,” inji Aderinto.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *