• Thu. Mar 28th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Duniya Ina Zaki Damu: Ga Matarsa Amma Ya Zabi Ya Yiwa Yar Cikinsa Fyaɗe

ByLucky Murakami

Aug 18, 2022

Wani magidanci ya zabi ya dinga kwanciya da yarsa duk da cewa shi ya haife ta kamar yadda muka samu labari.

Rahoton da amihad.com ta samu ya tabbatar mata da cewa: wata ýar kasuwa dake zaune a Ibadan, Misis Aminat Adeshina a ranar Litinin, 15 ga watan Ogusta ta bukaci wata kotun Ile-Tuntun, Ibadan da ta raba auren ta da mijinta Akeem Adesina na tsawon shakara 22 kan zargin neman lalata da ýar su.

A korafin ta, Amina wacce ked a ýaýa hudu t ace mijin nata ya yi yunkuin yiwa ýar su mai shekaru 16 fyade.

A cewar ta bayan ta bar gidan shi saboda rashin kula sai ya koma yunkurin lalata ýar su da ta bari a wajensa.

Da farko ýar tasu ta fada mata cewar wani ya shigo dakinta yana yi mata lalube a jiki, don haka sai washe gari ta fara tsine ma mutumin da basu san ko wanene ba a gaban mahaifin ta.

Amina ta ce ýar ta su ta fada mata cewa mahaifinta yayi kokarin siye ta da naira 1000.

Sai dai wanda ake karan bai ce komai ba akan zargin da ake masa. Yace matarsa ta yasar das hi lokacin da yake da tsananin bukatar ta.

Kan zargin kokarin yiwa ýar su fyade Adesina ya ki cewa komai.

Cif Henry Agbaje, alkalin kotun ya dage sauraron shari’an zuwa ranar 22 ga watan Ogusta inda ya bukaci da su kawo hujja domin marawa zarginsu baya.

Babbbar magana: Wani matashi mai shekara 27 zai kai iyayensa kotu saboda sun haife shi

A wani Al’amari me kama da Almara. Wani matashi mai shekara 27 zai kai iyayensa kotu saboda sun haife shi.

Wani mai shekaru 27 a kasar Indiya yana da shirin kai iyayensa kotu sakamakon haihuwarsa da suka yi.

Raphael Samuel dan asalin garin Mumbai ne kuma ya shaida wa BBC cewa ba daidai ba ne a ce an haifi mutum domin zai ta gwagwarmaya da wahalar duniya.

Amma Mista Samuel yana sane da cewa ba zai yiwu a nemi izinin mutum kafin a haife shi ba, amma ya dage a kan cewa “ba a nemi shawararsa ba kafin a haife shi.”

Ya bayyana cewa “Tun da ba mu ce a haife mu ba, ya kamata a biya bukatunmu har karshen rayuwarmu.”

Mista Samuel dai yana da wani irin ra’ayi wanda ke kyamatar haihuwa, masu irin wannan ra’ayi na Samuel suna kira ne da a dakatar da haihuwa saboda wahalar duniya.

Ya ce idan aka dakatar da haihuwa za a wayi gari babu dan adam ko daya a duniya kuma hakan zai kawo sauki ga wahalhalun duniya.

Ya ce “Babu wani alfanu a rayuwa irin ta dan adam. Mutane da dama suna shan wahala.

Idan ba dan adam a duniya, dabobbi da ita kanta duniyar za su kasance cikin farin ciki.”

Shekara daya da ta wuce, ya hada wani shafi a Facebook mai suna “Nihilanand,” wanda ke dauke da hotunansa dauke da gemu na karya, ya rufe fuskar sa, da kuma sakwanni irin na akidarsa da ke kyamatar haihuwa.

Mista Samuel ya shaida cewa ya fara irin wannan tunanin nasa tun yana dan shekara biyar.

Ya ce “Wata rana ina yaro, abin duniya ya dame ni kuma ba na so na je makaranta amma iyaye na suka matsa sai na je.

Sai na tambaye su: Me ya sa suka haife ni?’ Maihafi na bai da amsar da zai ba ni, sai na yi tunanin da ya amsa tambaya ta da ba zan ci gaba tunani haka ba.”

A lokacin da wannan akidar ta yi kamari a zuciyar Samuel, sai ya fito fili ya bayyana wa iyayensa irin wannan tunani nasa.

Ya ce iyayensa dukkansu biyu lauyoyi ne kuma a lokacin da ya bayyana masu abin da ke cikin zuciyarsa, sun yi na’am da wannan batu.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *