AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Home » Duniya Ina Zaki Damu: Wani Malamin Addini Ya Yiwa Wata ‘Yar Shekaru 8 Fyade
    News

    Duniya Ina Zaki Damu: Wani Malamin Addini Ya Yiwa Wata ‘Yar Shekaru 8 Fyade

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiAugust 21, 2022No Comments3 Mins Read
    Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email
    Share
    Facebook Twitter LinkedIn WhatsApp Pinterest Email

    Rahoton da yake shigo mana shine wani babban malamin addini ya shiga hannun hukuma inda ake zargi sa da yiwa yarinya aika-aika.

    Yan sanda sun cafke wani malamin addini, Pentecost Ewa Usang, a birnin Calabar a jihar Ribas a kan zargin yiwa wata ‘yar shekaru 8 fyade.

    Malamin addinin ya ce shi ke jagorantar cocin Christ Glorious Assembly a babban birnin jihar Ribas, Calabar.

    Ya fadawa manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda cewa aikin shaidan ne ya sa shi aikata wannan abun kunyar.

    Ya bayyana hakan ne mintuna kadan bayan kwamishinan ‘yan sanda resheh jihar Ribas, Mr. Mohammed Inuwa Hafiz, ya gabatar da shi a gaban manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda.

    “Ina nan ne a kan zargin bata budurcin wata ‘yan karamar yarinya, suna na Pentecost Ewa Usang, na kasance malamin addinin cocin Christ Glorious Assembly da ke Calabar.

    “Shaidan ne ya sa ni aikata wannan mummunar aiki kafin na dawo haiyaci na san abunda ni ke ciki na aikata aikin, ba ni na aikata wannan mummunar aikin ba.

    “Ina kusa da yarinyar sannan kafin abun ya faru, na dawo haiyaci na sannan ban bar abun ya faru ba, yarinyar ‘yar asalin kasar Kamaru ce,” ya ce.

    Sauran laifukan da suka shafi fyade da lalata budurcin mata inji kwamishinan ‘yan sanda, ya ce ya faru ne a unguwar Akamkpa inda wani matashi, Ubong Umoh, ya yiwa wata yarinya ‘yar shekaru 7, Victory Goodness Sunday.

    Dayan kuma ya faru ne a kauyen Edem Esa Abakot da ke Akpabuyo inda wani malamin addini cocin Jesus is Barrister in Zion Church, Daniel Asuquo Udoh, ya lalata budurcin wata yarinya ‘yar shekaru 7, Rachel Dominic, ta hanyar yi ma ta fyade.

    Kwamishinan ya ce ” a 22 ga watan Satumba, da misalin karfe 3:45 na yamma, wata tawagar ‘yan sanda da ke aiki karkashin ofishin ‘yan sanda da ke State Housig Division sun cafke wani matashi, Emmanuel Bassey, dan shekaru 35 wanda ake zargi da aikata fyade a gida mai lamba 35 a birnin Calabar bayan sun samu bayanin ya aikata fyaden.

    “Shi wanda ake zargi an samu labarin cewa ya dauke wata ma’aikaciyyarsa ‘yar shekaru 18, a wannan ranar da misalin karfe 8:300 na safe a gida mai wannan addireshen inda yayi amfani da iya karfensa ya yaga ma ta tufafinta sannan yayi ma ta fyade.

    “Yarinyar da aka yiwa fyade a nan take ba tare da bata lokaci ba aka garzaya da ita zuwa asibiti ‘yan sanda domin likitoci su duba lafiyar jikinta.

    Shi wanda ake zargi ya furta aikata laifin da ake zarginsa da shi sannan za a caje shi zuwa kotu da zaran ‘yan sanda sun gama gudanar da binciken su a kan lamarin,” Kwamishinan ya ce.

    Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email

    Related Posts

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    December 12, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022

    Yadda Aka Kama Malamin Addini Yana Lalata Da Yan Mata Biyu Yan Uwan Juna

    November 23, 2022
    Add A Comment

    Leave A Reply Cancel Reply

    Check Also

    Ya Kamata Kusan Da Wadannan Tsaruka Na Tallafi Da Ake Bawa Yan Nigeria

    January 27, 2023

    FG Begins SMEDAN ₦1.5m Loan – Application Portal

    January 20, 2023

    How to Obtain an Ecowas ePassport as a Holder of a Nigerian Passport

    January 20, 2023

    Easy Way to Apply for a Visa in Nigeria

    January 20, 2023

    Apply 2023 Microfinance Bank Kaduna Recruitment

    January 20, 2023
    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2023 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.