Labarin da mukaci karo dashi shine wani matashi a jihar kwara ya kashe mahaifinsa mai shekaru 90 a duniya domin ya samu damar mallakar asusun bankinsa.
Majiyar amihad.com ta rawaito cewa jami’an yan sanda na jihar kwara sun kama wani matashi mai suna ibrahim hassan,dan shekara 23 da lefin kashe mahaifinsa Sabi Ibrahim dan shekara 90,a layin Ajibesin kusa da Okolowo, ilorin saboda ya samu damar mallakar asusun bankinsa.
Mai magana da yawun kwamandan yan sanda na jihar,Sp Okansanmi Ajayi shiya tabbatarwa manema labarai da faruwar lamarin, inda yace a ranar 5 ga watan augusta ne wata yarinya mai suna Aisha ibrahim tazo ta fada masu cewa mahaifinta dan shekara 90 ya bace.
Yace bencike ya gudana inda aka kaiga kama Ibrahim wanda shine dansa mutumin na jini.
A yayin gudanar da benciken,wanda ake zargin ya tabbatar da ya hada allurar paracitamol da wasu sinadaran akan mahaifinsa, Wanda yayi lakwas ba yada karfi ta ke yanke bayan yi masa allurar,kuma yayi wannan ne bayan dawowarsu daga banki inda mahaifin nasa ya sabunta kuma ya karbo katin ATM dinsa.
Ya dauko mahaifinsa akan mashin sai yayi kokarin wucewa da mahaifin nasa keban taccen kango Wanda ba a ida ginawa ba,sannan yayi kokarin kashe mahaifin nasa ya mutu,ya gina rami ya binne gawarsa bayan ya charjesa ya dauki katin ATM dinsa Wanda sukaje banki suka anso kamar yadda Ajayi ya fada.
Jami’in dake magana da yawun yan sandan ya bayyana wanda ake zargin ya gudu jihar kaduna sannan ya cigaba da cire kudi daga asusun bankin mahaifin nasa daya mutu.
Ya cire kudi 59,000 daga asusun mahaifin nasa,Kuma ya bayyana cewa ya kashe mahaifinsa ne saboda ya dauki ATM dinsa tunda yasan pin dinsa.
Bugu da Kari Ya kuma saida mashin dinsa inda ya gudu jihar kaduna inda anan ne kuma aka kamashi, Katin ATM din da mashin din da ya sace an ganesu.
Ajayi “Ya kara da cewa zasu mikashi zuwa kotu nan bada dadewa ba.