• Sat. Jul 20th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Duniya Ina Zaki Damu Wata Mata Ta Tona Asirin Yadda Mijinta Ya Halaka ‘Ya’yansu

ByLucky Murakami

Sep 5, 2022

Wani labari da muka samu da dumi duminsa ya tabbatar mana da cewa wata mata ta tona asirin mijinta yadda ya halaka muku yara kamar yadda majiyar amihad.com ta tabbar.

Wata mata mai suna Laraba da ke zaune a jihar Adamawa ta tona asiri, kan yadda ta rasa ‘ya’yanta guda hudu a jihar Adamawa da mijinta mai suna Elisha Tari kamar yadda jaridar Leadership ta rawaito.

Wanda ya tabbatar da cewa shi ya kashe guda biyu daga cikin ‘ya’yan nasa hudu da aka kashe Elisha wanda a yanzu haka yana garkame a wajen ‘yansanda, ya bayyana wa manema labarai yadda wani mutum ya buga wa ‘ya’yansa guda biyu dutse aka, har suka mutu.

Elisha dai dan asalin kauyen Himike ne da ke karamar hukumar Michika, kuma an samu nasarar kama shi, bayan da aka sanar da ‘yansanda ya kashe ‘ya’yansa guda biyu, ta hanyar buga musu dutse.

Matar ta sa mai suna Laraba ta tsallake rijiya da baya daga hannun mijin nata bayan ya yi yunkurin kashe ta.

A tattaunawar Laraba, da ‘yanjarida ta ce, tana da ‘ya’ya hudu ta kuma yi bari sau daya tare da Elisha, amma biyun daga cikin ‘ya’yan sun mutu su kuma ragowar biyun ubansu ne ya kashe su.

Ta ce mijin nata yana shan wiwi da giya da tiramol kuma yana yin shake, ya zo bayan ta samu ‘ya’ya ya kashe su. Ta ce tana shan matukar wahala a hannunsa.

 

An Zalunce Ni Sama Da Naira Miliyan Daya Da Sunan Za’a Yi Mun Fim Ƙarkashin Kannywood

Labarin da majiyarmu ta samu daga jaridar dimokuraɗiyyar ta ruwaito cewa akwai wata sabuwa jaruma da anka laƙume ma kuɗi da niyar za’a yi mata fim amma babu labari.

Sabuwar jaruma a Masana’antar fina finan Hausa wato Kannywwod, Fa’iza Muhammad wadda ta shiga harkar a shekaru biyu (2) da suka gabata, ta bayyana irin wasa hankalin da aka yi mata wanda take jin ƙuna a duk lokacin da ta tuna da abinda ya faru.

Jarumar ta ce anyi mata wasa da hankali matuka, kuma an zalunce ta, ta hanyar karbe mata kudi da sunan za a yi mata fim amma ba a yi mata, aka yi watsi da ita, babu kudin babu fim.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu dangane da shigowar ta harkar fim.

Fa’iza Muhammad wadda ‘yar asalin Jihar Adamawa ce a garin Girei, ta ce ta yi aure tun a shekarar 2008 in da suka zauna da mijin ta tsawon shekaru 10 a Birnin jihar Edo, kuma sun samu yara 3 kafin daga bisani suka rabu, kuma daga baya Allah ya yi masa rasuwa.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *