Na kwanta da maza sama da 1,000,” in ji ma’aikaciyar Jima’i ‘yar Ghana.
Wata ‘yar Ghana mai shekaru 22 ta bayyana cewa ta kwanta da maza sama da 1,000.
Budurwar wadda shahararriyar yar rakiya ce a Ghana da aka fi sani da Gifty Osei aka Ohemaa Baddest, ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi da tashar talabijin ta SVTV Africa a baya-bayan nan inda ta yi magana kan sana’arta da ta yi a matsayin ’yar wasan raye-raye da jima’i.
A cewarta, ta rasa budurcinta tun tana shekara 10, kuma tun lokacin da ta daina tsafta a wannan shekarun, ta yi lalata da maza sama da 1,000.
“Ba zan iya ƙidaya ba, kimanin maza 1000 kenan, Babban abokina ta nuna min wannan aikin ban san ita ‘yar madigo ba ce, Mun kasance tare har tsawon shekaru hudu. Ita kadai ce yarinya da nake tare da ita.
“Wasu mutane takwas ne suka yi min fyade, suka kwashe kayana suka kore ni. Haka wani direban tasi ya yi, Kasuwanci ne mai haɗari, amma har yanzu ban yanke shawarar lokacin da zan daina ba saboda na kamu da shi, ”in ji ta.