• Sat. Jun 22nd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Duniya Tazo Karshe! Mata Sun Fara Tallen Lambobin Wayarsu Saboda Neman Mijin Aure

ByLucky Murakami

Aug 10, 2022

A wani bidiyo da mukai karo dashi ya tabbatar mana da cewa wata mata tana ikirarin cewa duk mai neman matar Aure Ya kira lambar wayarmu muna da fara da baka.

Wannan lamari ya faru cikin budiyon da matar ta sake a shafinta na sada zumunta wanda hakan ya bawa mutane mamaki matuka har ya jawo cece-kuce kan cewa nan gaba mata zasu fara zuwa don mika sakon soyayyarsu zuwa wajen maza.

Matar tace duk wanda ya kasance yana neman matar aure wanda bai taba aure ba ko kuma mai mata wanda yake son kara aure to maza ya kira lambar wayarta domin ta tanadi yan mata kala kala.

Tace tayi dogon nazari ganin yadda mata ke fama wajen neman mijin aure yayin da mazan auren kuma sunyi wahala a wannan zamani.

Kamar yadda amihad.com taji matar ta kuma kara da cewa duk kalar matar da mutum yakeso inma bahaushiya, bayerabiya, inyamura ko kuma ko wane yare da muke dashi a kasar nan to ta tanada yan mata kala kala sai wadda mutum yakeso.

Ta kuma ce suna da falani sirara da kuma masu kiba, gajeru da kuma dogaye, yan masu kudi da yayan masu rufin asiri, sai dai wadda mutum ya zaba.

Gadai bidiyon nan zamu gabatar muku a kasa don ji ta bakin wannan matar

https://www.youtube.com/watch?v=lGgvPf5wGNw

Sai dai kuma bayan bullar wannan bidiyo da yawa daga cikin mutane sunata maida martani inda wasu ke cewa wannan ai kamar cin zarafin aure ne. Idan mutum yanason aure yafi masa kyau yaje ya nemi mace ya hadu da ita gaba da gaba su tattauna don fahimtar juna.

Kazalika kamar yadda malamai suka fada akan irin wannan lamarin mutum baisan wace irin matar da zai dauko ba kuma zaman aure ba zamane na karamin lokaci ba, zamane na mutu ka raba musamman idan akwai soyayya ta gaskiya.

Muna rokon Allha ya hadamu da mata na gari ya kuma bamu zaman lafiya me dorewa.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *