Wani labari da mukai karo dashi mai ciem da al’ajabi cewa wani matashi da ya rankwala wa mahaifansa biyu tabarya ya kashe su, ya yi ikirarin cewa Jihadi ne abin da ya aikata.
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa shi dai wannan matashi ya shaida wa ’yan sanda cewa ya yi amfani da tabarwa wajen kashe mahaifan nasa ne saboda izgili da suke masa idan yana yin ibada.
Kamar yadda muka kawo muku a baya Idan baku manta ba Aminiya ta kawo rahoton wanann abin al’ajabi da matashin ya hallaka mahaifiyarsa Hauwa, mai shekara 60 da mahafinsa Ahmad Muhammad, mai shekara 70, wanda kuma shi ne Daggacin kauyen Zarada-Sabuwa a Karamar Hukumar Gagarawa ta Jihar Jigawa.
Bai tsaya a iya kansu ba, domin sai da ya rankwala wa kishiyar mahaifiyarsa mai shekara 50, Hakilima Ahmadu tabaryar da kuma wani makwabcinsu, Kailu Badugu, wanda dattijo ne mai shekara 65.
Tuni dai mahaifan nasa suka ce ga garinku nan, amma an sallamo kishiyar mahaifiyarsa daga asibiti, shi kuma makwabcin nasu har yanzu yana kwance magashiyyan a asibiti.
‘Dalilin da na kashe mahaifana’
Kakakin ’yan sanda na Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya shaida wa wakilinmu ta waya a ranar Asabar cewa matashin da ya yi wannan aika-aika, malamin makarantar Islamiyya ne.
DSP Lawan Shiisu Adam ya ce wanda ake zargin ya shaida musu cewa yana cikin hayyacinsa ya yi wannan aikata-aika da ya kira jihadi, kuma ba ya nadama.
“Malami ne a wata makarantar Islamiyya, hankalinsa lafiya kalau, ba ya ta’ammali da miyagun kwayoyi, domin ko goro ba ya ci.
“A lokacin da ’yan sanda ke masa tambayoyi, sai ya rika ce musu ai shi jihadi ya yi, jihadi ya yi, kuma shi a kan hanya madaidaiciya yake, su (wadanda ya kashe) ba mutane ba ne,” in ji Shiisu.
Ya ce matashin ya shaida musu cewa iyayen nasa sukan ce mishi mahaukaci a duk lokacin da yake yin wani abu na addini.
“Wannan na daga cikin dalilansa da ya bayyana wa ’yan sanda cewa sun sa ya kashe iyayen nasa kuma ba ya da na sani, ya shirya fuskantar kowane irin hukunci,” a cewar jami’in.
Allah ya kyauta ya shiryemu ya doramu kan tafarki madaidaici
Market
Wane irin akida yakebi wanda har takai idan yana ibada suna mashi dariya?