Rahotanni sun tabbatar da cewa, a cikin shekara biyu da suka wuce,iyaye 34 ne suka yi wa ‘ya’yan cikinsu 48 fyade, a cikin wasu bayanai da jaridar ‘Daily Trust’ ta ranar Lahadi ta tattara.
A wani bincike wanda majiyarmu jaridar Leadership tayi Jihar Legas ita ke kan gaba da mutum 11 sai Ondo 5, sai Ekiti 4, sai Kwara 3, sai Ogun ita ma 3, sannan sai Abiya da Anambura da Kano da Delta da Osun da Katsina da Edo da kuma Kuros Riba wadanda kuma kowannensu ke da daya.
Kamar yadda kididdigar ta nuan,daga cikin matsalolin 46 da suka faru, daya daga cikinsu jaririya ce, hudu kuma ‘yan kananan yara ne,sauran kuma kananan ‘yan mata guda 15.
Labari na baya-bayan nan da aka samu shi ne, a cikin watan Agusta, 2022, shi ne, na wani mai gadi mai kimanin shekara 55, mai suna Arowolo Ayodeji, ya yi wa ‘yarsa mai kimanin shekara 19 fyade a garin Ipoti da ke jihar Ekiti.
Da aka tambayi mahaifin yarinyar ko mai ya sa ya yi wannan danyrn aik? Sai ya ce, sharrin Shaidan ne, “Ba aikina ba ne.”
Mai magana da yawun jami’an tsaro na Sibil Difens (NSCDC) Olasunkanmi Ayeni, ya bayyana cewa, mutumin ya fara tursasa wa yarinyar tun tana ‘yar shekara bakwai.
“Wato zuwa yanzu ya shafe shekara biyu yana aikata wannan laifin ke nan,” In ji Mista Ayeni.
Ranar 19, ga watan Fabarairu 2022, haka kuma wani mutum mai shekara 28, mai suna Audu Dare, wanda ya yi wa ‘yarsa fyade mai shekara 6, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta, sakamakon haka aka tsare shi a Ado Ekiti.
Matar da Dare ya ci gaba da bibiya wata mai suna Eniola Aina, wadda ta ce sun taba yin aure a shekarun baya, kuma har ma sun haifi da namiji amma sai suka rabu, shekara hudu da suka wuce sakamakon wasu munanan halayensa.
“Bayan rabuwarmu, wata rana, sai ya zo gidana da ke garin Ilawe Ekiti ya ce, zai karbi ‘yarsa, ni kuma na ce, ba zan ba shi ba, sai ya dawo da misalin karfe 12 na dare ya sace ta”.
“Bayan ‘yan kwanaki kadan sai yarinya ta fara kukan ciwon kai sannan kuma ta ce mafitsararta na yi mata zafi. Nan da nan aka kai ta wani asibiti da ke kusa da su, a nan ne ta gaya min cewa, babanta ya yi mata fyade wanda kuma hakan ta yi sanadiyyar mutuwarta.”
Haka kuma a wani makamancin wannan an kama wani mutum mai ‘ya’ya shida, mai suna Sunday Julius, yana lalata da kananan ‘ya’yansa guda hudu, daya mai shekara bakwai da mai shekara 10 da wata mai shekara 11 da kuma wata mai shekara15, a jihar Legas.
Julius, ya ce yana zaune da iyalansa ne a wata unguwa da ake kira Alimosho da ke jihar, kuma matarsa ta sha kama shi da yaran.
“Mun yi aure a shekara ta 2007 kuma mun haifi ‘ya’ya shida tare”.
“Yarmu ta farko mai kimanin shekara 15, ta sha gaya min cewa, da zarar sun kwanta da daddare sai ya lallabo wajen da take kwanciya,ya fara amfani da ita”.
“Haka yake binmu, mu hudu daya bayan daya, idan muka ki ya tursasa mana dole”.
“Ya kan shigo dakin namu ne cikin tsakiyar dare yayin da muke cikin bacci. Yana kuma tsorata su da zarar ya ga alamar ba za su yar da ba. Muna kwanta tare da dare ya yi, sai ya kashe wuta, ya lallaba ya tafi inda yarinyarmu mai shekara 10 ke kwana, ya je ya sadu da ita.
Sai da gari ya waye, na gaya masa cewa, na gan shi yana lalata da yarinyata, ya ce, karya nake yi masa. Saboda haka kwana hudu sai na daina yin girki sai ya yi fushi har yana dukana,” matar mai shekara 36, wadda ke sasayar da magungunan gargajiya ta ce ita Bayarabiya ce.
Babbar ‘yar mutumin mai shekara 15, wadda a halin yanzu take sakandire, ita ta tona asiri, wadda ta ce babanta yana saduwa da ita duk loacin da ta dawo gida daga makaranta. Ta ce, “Ina son in tube kayana lokacin da baban yake shigo wa. Domin yana kwantar da ni a gado, yana saduwa da ni”.
“Lokacin da yake saduwa da ni, sai kanwa ta, sai nan da nan ya daga ni. Sai take tambaya menene yake faruwa sai na yi mata. Ita kuma sai ta gaya wa babarmu. Sai babarmu ta ce, ai ni ce da laifi da ban gaya mat aba tun da wuri. Sai na ce mata ni ina jin tsoron gaya mata ne, domin baban nawa ya ce in na gaya miki zai kashe ni.”
Ashe ni ban san a
kwai wasu ‘yan uwan wannan yarinyar guda biyu da yake saduwa da su ba, daya mai shekara 7 da kuma mai shekara 11 wadanda suka ce babansu na tursasa musu har sai sun sadu da shi da daddare kuma ya ja musu kunne cewa, kada su sake su gaya wa wani. Daya daga cikinsu mai kimanin shekara 10 ta ce “Babana yana tursasa mini da daddare.”
Da aka tambaye su mai ya sa ba su fada ba tuntuni, sai suka ce, baban nasu ne ya ce, kada su kuskura su fada wa kowa.
Haka kuma a wata makamanciyar wannan da ta faru a garin Ile-Oluji da ke jihar Ondo, an kama wani dansanda mai suna Sunday Udoh, mai shekara 38, yana kokarin tursasa wa ‘yarsa ta zubar da cikin da ya yi mata.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Ondo Funmilayo Odunlami, ya bayyana haka, sannan kuma ya tabbatar da cewa, tuni sun kama wanda ake zargin, kuma yanzu haka yana garkame a hedikwatar ‘yansanda da ke Ile-Oluji, wanda kuma ya nuna inda aka zubar da cikin.
“Lokacin da ake bincike an gano cewa, matar wanda ake zargin wadda aka sakaya sunanta ta bukaci a zubar da cikin ‘yartatata mai kimanin shekara 15 wadda ta samu daga mahaifinta.
“Yanzu haka dai an mika wannan bincike zuwa sashin binciken manyan laifuka da ke Akure,” in ji shi.
Mako guda kafin wannan lokaci ‘yansanda a jihar sun kama wani uba mai kimanin shekara 27 mai suna Adeniyi
Adeleke, bisa zargin yi wa ‘yarsa fyade mai kimanin shekara 10.
Haka kuma ‘yansanda sun nuna Mista Adeleke da wani mai shekara 46 mai suna Jimoh Rafiu wadanda suka yi wa yarinya mai shekara shida fyade.
Sannan ta nuna mikin da daya daga cikinsu ya yi mata lokacin da yake kokarin saduwa da ita.
Mahaifiyar yarinyar ta ce, duk lokacin da ta dawo daga wajen aiki, sai kawai mijin nata ya cire wa ‘yarsa kayan jikinta, ya ce, yana bukatar ya sadu da ita.
Bayan da ta fara jin ciwon mara da kafafrwanta sai ta gaya wa babarta, sai babartata, ta je wajrn mijin nata, sakamakon jin wannan labara.
Daga nan sai ta kai kara gurin dattawan gari inda suka kira shi, suka gurfanar da shi, a nan ya yi alkawarin cewa, ba zai sake yin haka ba.
Bayan ‘yan kwanaki, sai yarinyar ta samu sauki, daga nan ne sai uwar yarinyar ta kai kara ofishin ‘yansanda da ke Jimoh.
A nan ma Jimoh ya tabbatar da aikata laifin da ake zarginsa da shi, na yi wa matarsa fyade lokacin da ya sha giya. Mutane da yawa sun yi mamakin yadda wannan mutum ya fada tarkon s
haidan.