• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Gaskiya 10 Daya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Tsarin Kamfanin NNPC

ByLucky Murakami

Jul 20, 2022

Mun mayar da kamfanin NNPC hannun ‘yan kasuwa cewar shugaba Buhari. Ga gaskiya 10 daya kamata ku sani akan wannan sabon tsari.

1. NNPC anyi “Commercialising” nasa, ba privatisatizing” nasa aka yiba.

2. Akwai banbanci sosai tsakanin “Privatization” da Commercialization”

3. “Privatisation” yana nufin sayar da kadara ko kuma kamfani mallakar gwamnati zuwa ga yan ‘kasuwa.

4. “Commercialization” yana nufin canja gudanarwar kamfani mallakar gwamnati ya koma ana gudanar da shi lamar yadda ake gudanar da kamfani na yankasuwa, ja tare da an sayar da shiba.

5. Shi NNPC Limited gwamnatice zata ci gaba da gudanar da shi saboda ita ta mallaki 100%.

6. Gudanarwar zata kasance a sabon tsari kamar yadda ake gudanar da kamfanunuwan ‘yan kasuwa (domin samun riba).

7. Nan gaba kuma idan taga dama zata iya siyarwa da yan kasuwa hannun jari domin shigowa cikin gudanarwar, kamar yadda akayi a NLNG, Gwamanti tana da 49%, yan kasuwa suna da 51%. (Shell Gas B.V. suna da 25.6%, Total LNG Nigeria Ltd suna da 15% sai kuma Eni International suna da 10.4%.)

8. Misalin Saudi Aramco (Shine kamar NNPC na Saudi Arabia) gwamnatin Saudia tana da kaso 98.5% su kuma yan kasuwa suna da 1.5%.

9. Ethiopian Airline, shima commercialised company ne wanda gwamnatin Ethiopia take da 100% ownership (Kamar NNPC a yanzu) kuma take gudanar da shi domin riba.

10. Akwai misalai da dama a kasashen Africa, Asia, Middle East da sauran bangarori na duniya.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *