• Sat. Oct 12th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Gaskiyar Abinda Ke Mata Zaman Aure Babban Asiri Ya Tonu

ByLucky Murakami

Oct 3, 2022

Mutane da yawa sukan zaci cewa yawan mata a duniya shi yasa wasu daga cikin su suke rasa miji. Zaton jama’a da yawa shi ne mata sun fi maza yawa a duniya.

Shi ya sa zaka ji wasu suna cewa ko da duk mazan duniya za su auri mata hudu hudu, toh wasu za su rage. Har ma sukan yi ikirarin tabbatuwar hakan a addinance da cewa mata a karshen duniya za su ninka maza. mai yiyuwa hakan zai faru a nan gaba in duniyar tazo karshe.

Amma a halin da ake ciki yanzu, maza su ne suka fi mata yawa a duniya domin kididdiga da akayi na mutanen duniya ya nuna yawan maza ya kai kusan kaso 51 a duniya yayinda na mata ya dauki kashi 49 da wani abu.

Hakazalika, ko a kidayar da aka yi a Nijeriya a shekarar 2006 ya nuna cewa yawan maza da mata a najeriya kusan daidai ne duk da cewa maza su suke da rinjaye da lambobi kadan.

Abin da yake jawo yawan mata marasa aure ba wani abu bane face al’adun mu na auren kannen mu a matsayin matan mu. Ma’ana kowa baya auren mace sa’ar sa sai wacce ya girme ta.

Hakan yasa muke tsallake sa’annin mu mu auri na kasa da mu. Kaga in kowa ya tsallake sa’annin sa, dole su zamo ba mazaje har sai sun samu wadanda suka girme su suma.

Kenan in kowa zai auri wacce ya girma ne, toh dole a cigaba da samun mata marasa mazaje sai dai in mutum zai rinka auren fiye da daya. Amma bawai mata sun yi yawa bane cikin al’ummah kamar yadda ake zato.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *