Wasu hotuna da suketa yawp a shafukan sada zumunta wanda mutane suke ta cewa akwai yiyuwar mawaki Ado Gwanja zai auri jaruma Momee Gombe. Tirkashi, menene gaskiyar wannan lamari?
A binciken da amihad.com tayi ya tabbatar mana da cewa wannan jita-jita ta samo asali ne bayan ganin shi mawaki Ado Gwanja ya wallafa hotunansa tare da Momee Gombe a shafinsa na Instagram.
Kamar yadda zamu kawo muku wannan abu daya wallafa a hoton dake kasa wanda wallafa a kasa ya rubuta “Time” sannan yayi tagin na sunan wannan jaruma.
Bayan ganin wannan abu da mawaki Ado Gwanja ya wallafa wasu mutane a shashen ajiye ra’ayi sunyi tayashi murna wasu kuma sun gane inda abin ya dosa.
Maganar gaskiya a nan itace babu wata tabbatacciyar magana ta aure tsakaninsu zuwa wannan lokaci da muke kawo muku wannan rahoto. Sai dai bamu san abinda zai biyo baya ba.
Wandan nan sune hotunan da shi mawaki Ado Gwanja ya wallafa wanda suka jawo wannan cece-kuce.
A karshe muna tabbatar muku da cewa amihad.com zataci gaba da bibiyar wanannan lamarin domin gano gaskiyar zance. Ko kuma idan aka samu wata magana data tabbatar to zamu kawo muku ita. Kuci gaba da kasancewa tare damu domin samun labarai da dumi duminsu.