Akwai labarin da yake yawo a kafafen sada zumunta wanda ke nuna wani hoto na fitacciyar jarumar kannywood Maryam Booth tare da wani da mutane suke cewa shine mijin da zata aura.
Binciken da amihad.com tayi ya tabbatar da wannan labari ba gaskiya bane, saboda haka ku gyara zama domin jin gaskiyar labari.
Jarumar Kannywood, Maryam Booth shafinta na Instagram ta wallafa hotonta da wani wanda binciken mu ya tabbatar mana cewa jarumin fina finan kudu ne a jikin hoton ta rubuta: ‘Mr and Mrs yusuf’.

Wannan hoto data saka ya sa masoyanta sukayi ta maganganu kal-kala a shafukan sada zumunta musamman na arewacin Najeriya.
Gaskiyar magana itace wani sabon shirin fim ne da suke dauka wanda zata fito a matsayin wannan jarumi mai suna Akeem Adeiza wannan sanannen jarumi ne.
A gefe guda kuma hotunan dai ya jawo martani da dama daga masoyanta a shafinta na Instagram, yawancinsu sun yi mata murna sosai kuma suna taya ta murna yayin da take shirin shiga wani babi na rayuwarta amma fa a shirin fim.
Sai dai a shashe na ajiye ra’ayi ita jarumar tabi mutane masu tayata murna tana fada musu gaskiyar lamari akan wannan ba hoton aurenta bane wani sabon shiri ne wanda suke kan daukarsa yanzu.
Kuci gaba da kansancewa da amihad.com domin samun sahihan labari na yau da kullum.