Jami’an tsaro sun kama wata mata da ake zargin ta saci jariri sabuwar haihuwa, Ibrahim Khalid a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
Jaridar Punch ta ce jaririn wanda ɗan tagwaye ne, an sace shi ne ranar Talatar makon jiya a dakin asibiti, kafin a gano tare da mayar da shi hannun mahafiyarsa.
Ana zargin wacce ta saci jaririn da yin shiga kamar ma’aikaciyar jinya a asibitin kuma ta lallaba ta zari yaron ba tare da an kama ta ba.
Bayanai sun ce wadda ake zargin ta sace jaririn ne saboda damuwar da ta shiga sakamakon yawan gorin da dangin miji ke yi mata na rashin haihuwa.
Wadda zargin ta kai jaririn kauyensu na Dull a cikin karamar hukumar Tafawa Balewa tana cewa dan da ta haifa ne.
Da a ke tuhumar ta, sai matar ta kada baki ta ce ta na shan horon rashin haihuwa ne shi ya sanya ta aikata wannan aika-aika.