Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Family & Relationships

    Hanyoyi 5 Da Mace Zata Mallaki Miji Cikin Sauki

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiAugust 16, 2022No Comments4 Mins Read

    Kamar yadda kuka sani yana daga cikin halayyar mata, neman hanyar da su mallaki miji. Irin wannan lamari kan ba wasu mata matsala wajen gane yadda za su bi su mallaki miji cikin sauki.

    Wasu daga ciki gani suke, zuwa wurin boka ko malam a samu wasu siddabaru a matsayin taimako domin mallake miji shi ya fi sauki.

    Mata ga hanyoyi mafi sauki na mallakar miji wanda aka tsara bisa koyarwa manzo:

    1. Ya kasance duk magana da zai fita daga bakinki mai dadi ne a kunnen mijinki wanda zai sa shi murmushi da jin dadi.

    2. Ki kasance a kullum kin dauki mijinki tamkar sarki ne ta wurin mutunta shi, da juriya wajen daukar laifinsa ya dawo kanki saboda bashi girma ko da ke ce da gaskiya.

    3. Ki kasance mai sakin fuska ga mijinki a duk lokacin da ya shigo gida ya same ki cikin frinciki ko da akasin haka ne.

    5. Kar ki kasance kullum a cikin bacin rai ko fushi da mijinki, domin fushi shi ne kofa na kowane sharri.

     

    Matsalolin Kishiyoyi Da Yadda Za A Magance Su

    – Tambaya

    Matambayi: Don Allah mallam menene yake kawo matsaloli tsakanin kishiyoyi, saboda ina son na kara aure?

    – Amsa

    Mallam Sa’idu Kankia: To malam Kishi wata dabi’a ce da Allah ya halicci mata akanta, Nana A’isha tana cewa: “Ban taba yin wani kishi ba, irin kishin da na yiwa Khadijah, duk da cewa ban taba ganinta ba, saboda yadda na ji Annabi S.A.W yana ambatonta”

    Bukhari 1388 Kishi mai tsafta, shi ne: kishiya ta yi rige-rige da kishiyarta, wajan kyautatawa mijinsu, za mu iya mayar da abubuwan da suke kawo kishi mara tsafta zuwa abubuwa guda hudu, wadanda in har da za su warwaru, to da ka ji dadin zama da matanka, saboda za su zama kamar ‘yan biyu:

    1. JAHILCI: Ta yadda mata da yawa suka jahilci, hikimomin da suka sa Allah ya yi umarni a kara aure, kamar : rage yawan zawarawa da ‘yammata, da kuma yawaita zurriyar Annabi s.a.w., domin da za su kalli wannan da kishinsu ya ragu.

    2. MUMMUNAN ZATO: Yawanci uwar gida tana tarbar amarya da mummunan zaton cewa za ta rainata, haka ita ma amarya ta kan zo da mummunan zaton cewa ba za su yi zaman lafiya ba da uwar gida, wannan sai ya sa daga zarar sun hadu babu wuya sun yi rigima.

    Amma idan da ace kowacce za ta tarbi kowacce da kyakykyawan zato, har ta ga kamun ludayinta da ba’a samu matsala ba.

    3. RASHIN ADALCI DAGA WAJEN NAMIJI: Yawanci maza su kan karkata zuwa amarya, wannan sai ya haddasa fitina, saboda uwar gida za ta ce ba ta yarda ba. Saidai abin da ya kamata mata su fahimta shi ne:

    Babu yadda za’a yi namiji ya hada mata biyu face sai ya fi son daya, Annabi S.A.W ya zauna da mata tara kuma ya fi son Nana A’isha, har ma mutane sun fahimci haka, wannan ya sa idan za su yi masa kyauta.

    Sukan kirdadi ranakun da yake dakinta, don sun san kyautarsu za ta fi karbuwa a ranar, don haka idan kika ga mijinki ya fi son kishiyarki, ki yi masa uzuri kar ki tada fitina, saidai abin da sharia ta hana shi ne : rashin adalcin ya fito a hidimomin yau da kullum.

    4. MUNAFUKAI MASU CECE-KUCE: Idan da ace kishiyoyi za su daina daukar guzuri-zoma, ta yadda idan suka ji magana za su tabbatar da ita kafin su yi hakunci ga kishiyarsu da hakan ya rage kawo matsaloli.

    IDAN HAR WADANNAN MATSALOLIN ZA SU WARWARE, INA GANIN ZA A SAMU KISHI MAI TSAFTA.

    Ma'aurata Mata Da Miji Rayuwar Aure Soyayya

    Related Posts

    Yadda Kanin Miji Ya Dirkawa Amaryar Yayansa Ciki A Nasarawa

    November 19, 2022

    Sati Biyu Kacal Da Yin Aure Amarya Ta Bukaci Ango Ya Saketa Saboda Baya Iya Gamsar Da Ita A Kan Gado

    November 18, 2022

    Yadda Ake Kwalliyar Maida Tsohuwa Yarinya

    November 7, 2022

    Lokuta Da Yawa Maza Yan Iska Sunfi Iya Soyayya Wata Budurwa Ta Kira Ruwa

    November 5, 2022

    Yadda Ango Yayi Dawowar Bazata Ya Kama Matarsa Da Babban Abokinsa Suna Cin Amanarsa

    November 4, 2022

    Bidiyon Hira Da Matar Da Take Auren Maza Biyu Kuma Suke Kwana Kan Gado Daya

    November 3, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.