• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Hattara Masu Neman Aure Ga Abubuwan Da Ake Fasa Aure Saboda Su

ByLucky Murakami

Sep 30, 2022

Assalamu alaikum, da fatan malamai da dukkan ‘yan’uwa sun tashi lafiya. Ina rokon Malam ya yi mana bayani kan shin wadanne abubuwa ne ake iya fasa aure saboda su, domin akwai wanda aka sanya ma ranar aure kafin lokacin ya ce ya fasa?

Allah ya kara wa malam lafiya da basira, Amin Wa alaikum assalam, in har akwai hujjar da shari’a ta yadda da ita, ba shi da laifi in ya fasa, kamar ya bayyana budurwar ta sa ba ta da tarbiyya ko mazinaciya ce, ko kuma ba ta son shi, ko tana da cutar da za ta hana a sadu da ita, kamar toshewar farji ko hadewarsa da dubura, ko ya zama su duka suna da jinin da in sun hadu za su haifi sikila, yana iya fasa auren idan ya zama ba shi da halin da zai iya ciyar da ita, ko kuma likita ya tabbatar masa ba shi da mazakutar da zai iya saduwa da mace, haka ma idan ya ji ya tsane ta.

Dukkan abin da ake iya saki saboda shi, ana iya fasa aure ın aka same shi, an shar’anta saki ne saboda tunkude cuta daga ma’aurata ko daya daga cikinsu, yana daga cikin ka’idojin shari’a da kuma masu hankali: Tunkude cuta kafin ta auku, ya fi sauki fiye da kokarin kautar da ita bayan ta faru. Allah ne mafi sani.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *