Labarin da kafar Amihad.com take samu shine wani karamin yaro dai ya taso tun daga jihar Adamawa har kano inda yace yazo gurin ado gwanja yace shi cikakken masoyin sani yanajin wakokin sa da kuma fina finan shi tunba yanzu.
Wanda hakan yasa ya taso tun daga jihar Adamawa yazo garin Kano domin ya hadu da mawaki kuma Jarumi Ado Gwanja.
Yazo domin haduwa da ado gwanjan kuma sun hadu inda akaga bidiyon haduwar tasu yana yawo hakan yasa hukumar hisba bankado inda yaron yake domin kamasi kuma su mayar da shi gurin iyayenshi a jihar adamawa.
Yanzu dai yayin faruwar haka ake inda akwanakin baya wani yaro yazo tun daga Niger gurun mawaki Ali jita domin nuna soyayya a gareshe.
[ads1]
Hukumar hisba dai ta kama yaron inda suka tambayi daga inda ya fito yace shi ɗan jihar Adamawa ne kuma yazo ne gurin ado gwanja domin ya nuna masa irin soyayyar da yake masa.
Hukumar ta hisba ta mayar da wannan yaron izuwa mahaifarsa dake jihar Adamawa.
Ga bidiyon rahoton abinda ya faru:
Sai dai anji ta bakin ado gwanja inda yace shifa yana maraba da duk wani masoyansa daga ko ina suke a fadin duniya yayin ziyarar da yaron yazo dai ado gwanja ya bawa yaron kyautar kudi da kayan sawa.