Wani Magidanci Kenan Da Ya Yi Hotunan Murnar Sallah Tare Da ‘Ya’yansa 19 Da Matansa Uku
Wani ‘dan Najeriya yayi shagalin bikin sallah babba inda har ya bayyana hotunansa tare da matansa uku reras da ‘ya’yansa 19.
Bawan Allah mai suna Baba Lawal, ya wallafa kyawawan hotunan ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yulin 2022 a shafinsa na Facebook.
A hotunan sun yi ankon kaya kalar kasa mai duhu yayin da matan suka saka hijabai kalar kayan mijinsu da ‘ya’yansu sannan suka sanya niqabai a fuskokinsu.
Lawal, wanda ‘dan asalin jihar Kwara ne, yana koyarwa a kwalejin ilimi ta Umar Bn Khattab dake Kaduna kuma shine sakataren hukumar Hisbah na jihar Kaduna kamar yadda bayanansa na shafinsa a Facebook suka nuna.
Ga jerin hotunan nasu akasa tare da Iyalansa
Allah ya ba shi ikon daukar dawainiyarsu.