Ana sabanin ra’ayi kan malamar da tace in mijinki Ya mareki ki sumbace kece I love you habibi
Wannan bidiyon na malama ya jawo cece kuke wanda malamar tayi hakan domin kwantar da hankalin mijinki wanda kowa yasa yanzu mutuwar auren matar bahaushe ba komai bane.
Wanda anka samu wasu sun goyi bayan hakan wasu kuma basu goyi bayan hakan ba.
Ga bidiyon nan domin jin yadda ta kaya
Illolin Rashin Yi Wa Miji Biyayya
Aure wata bauta ce ta ubangiji kuma sunna ce mai karfi ta Manzon Allah (SAW). Don haka wajibin kowacce mace ce da ta tsinci kanta cikin rayuwar aure ta yi riko kwarai da igiyar aurenta tare da yi wa mijinta biyayya kamar yadda shari’a ta gindaya.
Ko daga halitta Allah ya fifita namiji a kan mace, kama a gangaro kan wasu abubuwa da su ka shafi addini kamar walicci, gado da dai sauransu.
Idan kuwa haka ne ashe ya zamar wa mata tilas yin biyayya ga mazajen aurensu, domin su na karkashinsu ne. Ko a al’adance ce idan za a aurar da yarinya za ka ga kakanni, iyaye an ajiye amarya a na ce ma ta “Yi Na Yi, Bari Na Bari Shi Ne Aure”.
Hakan ba wani abu ke nufi ba face lallai ne mace ta bi dokokin aure tare da yi wa miji biyayya a kan abinda ya shimfida ma ta matukar bai keta dokokin Allah ba.
Misali; wajibi ne mace ta kula da amanar mijinta ya na nan ko baya nan, kama daga tsare mutumcin kanta, gidansa, dukiyarsa, ’ya’yansa da duk wani abu nasa.
Haka zalika fita, lallai mace ta tsare kafafunta daga fita ba tare da izinin mijinta ba, ta kula ma sa da tarbiyyar yaransu, ta zama idonsa a kan komai. Sannan kar ta dauki abincin gidansa ta siyar ko kyautar ba tare da saninsa da amincewarsa ba.
Idan a ka ce yiwa miji biyayya abu ne da ya shafi abubuwa da dama na cikin aure, kama daga kan sauke hakki na aure ya zuwa sauran mu’amulolin rayuwa.
Sauke hakki na aure shi ne biyawa miji bukatunsa yadda ya kamata, inda za ki kare shi daga fita ya fada wasu hanyoyi marasa kyau.
Ki kuma zama mai tsaftar jiki, gida da lafuzza masu tsafta da kosar da mijinki abinci a kan lokaci, domin sau tari wasu matan kan bijirewa mazajensu dokokin da su ka dora su a kai na tsafta, girki da dai sauransu, fafur namiji ya ce ga lokacin da ya ke so mace ta gama girki ta ki ko ga lokacin da ya ke so ki yi wanka, nan ma ki ki, ko ga lokacin da ya ke so ya kasance da ita, nan ma ta bijire, wanda duk ire-iren wannan mata mu bar raina su, su na daga cikin tsantsar rashin tarbiyya da rashin biyayya ga maigida.
Abin da mata da yawa su ka kasa ganewa shi ne, rashin yi wa mazajen su biyayya babban nakasu ne ga rayuwarsu, haka kuma danasani ne sakamakonsu.
Manyan illolin da mace za ta fuskanta sakamakon rashin biyayyar kuwa su ne:
A wajen ubangiji sakamakonki na nan da a ka tanadar wa mace wadda ba ta yi wa mijinta biyayya kamar yadda Shari’ah ta shimfida, kuma mu sani aljannar mace na karkashin tafin mijinta ne.
A wajen al’umma mace maras kimanta da daraja mijinta, sam ba ta da girma da daraja a idanun mutane, face kallo na banza da rashin kima da Allah wadai da ta ke samu tare da zunden ta.
Ko a makwaftanta ba ta da wata kima da daraja, yayin da matan makwaftanta za su yi nesa da mu’amala da ita, saboda jan kunnen da mazajensu za su gindaya ma su a kan mu’amala da ita, don gudun kar ta bata mu su rayuwa.
Ga dangin miji kuwa ko iyayensa za ta kasance a bar zagi, tsana da tsangwama tare da rashin girma ko mutunci a idonsu, wanda hatta ’yay’an da ta haifa sai wannan bakin jini nata ya shafe su. Idan kishiya ne da ita kuma za su so da kaunar kishiyar tata fiye da ita.
Haka idan ’ya’ya mata ne da ita, tabbas ta gama cutar da su, ta bata mu su tarbiyya domin abinda su ka ga ta na yi wa mahaifinsu, haka su ma za su dauka su rike, ranar da duk a ka aurar da su, su je su baza kolin halayyar a gidaden aurensu, wanda idan ba a yi wasa ba a koro su, domin ba kowanne namiji ke da hakurin jure rashin biyayyar mace ba.
Kai kafin a kai ga auren ’ya’yanki, sai an yi da gaske za su sami miji, domin da an zo neman aurensu, cikin unguwa za a zuge masu neman auren wajen sanar masu cewa yaran uwarsu ba ta da tarbiyya tare da zayyana miyagun halayyar uwar ga masu auren.
Shi kuwa mijin da ki ke yi wa wannan rashin albarkar, to ki sani sam babu zancen son ki a zuciyarsa, illa kawai ya na hakurin zama da ke ne saboda Allah ko saboda yaranku ko iyayenki, kuma duk ranar da ki ka kai shi bango, ya rabu da ke, to ba zai sake waiwayarki ba, domin ya jefar da kwallon mangwaro ne ya huta da kuda.
Sannan rayuwarki ta shiga garari kenan, domin babu mai aurenki, don ko wani ya zo cikin rashin sani, tabbas za a zagaya a wassafa ma sa halayenki tas marasa kyau, wanda su kai yo waje da ke daga gidan tsohon mijinki.
Malllakar Miji, Biyayya Ko Sihiri?
“DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI!” biyani a kan wannan abu ukun wato MIJI SIHIRI DA KUMA BIYAYYA
1. Miji a fada tasa ma’aikin Allah annabi muhammad (saw) yace- “da ace zan umarci wani yayi wa abun halitta sujjada dana umarni mace taiwa mijinta” wannan bayani na ma’aiki (saw) baya nuni da komai face tsananin girman miji da kuma hakkin dake kan mace nayi masa BIYAYYA.
A mahanga ta biyu kuma wata a zamantakewar ce na musulunci ko sauran addinai an hadu kuma an tafi a kan cewa miji shine jigo kuma jagoran kowa ne iyali wanda kowace mace ke takama da a ce tana jagoran gidansu ubansu ne mijin mahaifiyarsu.
2. SIHIRI- shine duk wani kulli da surkulle da za kayi ka kauda mutum daga tunaninsa ya rika abu ba a kan ra’ayi da cikin hankalinsa ba a mahangar addini, tun daga musulunci har izuwa sauran addinai da suke ahlus-kitabi sun hadu sun tafi a kan cewa sihiri haramun ne duk da musulunci ya tabbatar da cewa mai yi da mai zuwa don ayi masa sihiri mushrikai ne to amma su ma sunyi ishara da cewa duk mai sihiri da mai zuwa gunsa to batattu ne kuma sun butulcewa Allah (swt).
Sai mahanga ta zamantakewa hakika tun da addini musulunci ya mamayi kasar hausa ya rufe babin sihiri da tsafi wannan tasa masihirta da masu bibiyarsu suka zama abin kyama har ga wadanda ma basu da cikakken ilimi na islama domin zuwan musulunci ya wayar dasu cewa wannan abin fa ba wurin alkhari bane
3. Abu na uku shine BIYAYYA wato kalmar biyayya tana nufin kyautatawa da kokari wajen aikin da zai farantawa wanda kakewa biyayyar rai yazo a hadisi annabi(saw) yace an gina zuciya a kan son wanda ya kyautata mata da kin wanda ya munana mata”.
Wannan ishara ce garemu cewa zuciyar mutum bata samuwa da komai sai biyayya da kyautatawa karamin misali
shine ga gabbobi zakaga dan adam ya ajiye dabba mai hastari a gidansa amma bata cutar da shi
saboda fahimtar abin da takeso da yayi kuma yake kokari wajen aikatawa, wato yana biyayya ga abin da take so itama wannan kenan.
Ko kun lura da cewa mutanen yanzu sunfi mutanen da wadatuwa da ilimin addini da wayewa sakamakon a da zakaga kan mutum ya samu ilimi sai ya sha wahala wani har ta kai shi ga barin mahaifarsa, don haka sai kaje gari guda kaga malaman garin basu fi ka kirga da yatsun hannunka ba.
Sabanin yanzu da a unguwa daya kawai sai ka samu malamai sun kusa rabin jama’ar cikinta sakamakon saukin da aka samu ta fannonin rayuwa.
Amma abin mamaki mutanen yanzu sunfi nada dulmiya a kan aikin sabo wanda ya hada har da shirka mafi munin zunubi a gurin ubangiji daga cikin masu bada himmar wannan abu shine yan’uwa mata hakika mata sun nutsa a wannan bakon al’ada ba domin rashin ilim ko wayewa ba, a’a tsabar shaidan dake kada musu gangar halaka dabata da kuma son zuciya.
Shin meke jan hankalin mata a wannan bakar dabi’ar a iya bincikena na gano cewa kaso 99 a cikin 100 na matan dake ziyartar wajen boka ba wani abu ke kai suba face su.
“MALLAKI MAZAN ” ta yanda ba zai iya mata musu ba ga duk abin da take so bare ya kai ga yi mata kishiya!
Tabbas bakin kishi ya dauki mata ya tsunduma a tekun halaka mai girma da zurfi yanda ta kai suna iya komai domin hana miji ya kara aure har takai tun ana yi a boye a yau ta kai ta kawo a bayyane ake tallan wannan bala’i
ga duk mai-tu’ammali da zaurukan sada zumuta musamman.
“WHATSAPP” yana da sanin ire ire wannan abubuwa da ake yadawa da sunan “MALLAKAR MIJI” daya daga ciki shine wani surkulle da ake hadawa da kashin tattabara ayi tsarki da shi da sunan cewa duk matar data yi wannan ba mijinta ba kallon wata mace kuma bare har yaji dadin mu’amakar aure da ita.
Tafi tafiya a yau har ta kai cewa wai ana tallan wani zanin gado da zanin daurawa shi zanin gadon in namiji ya kwanta kai ya sadu da matar, ba zai taba daban wata ba kuma shi zanen daurewar aljana ke jikinsa in ta daura mijin ya kwanta da ita shike nan ba shi ba aure ko da yana dashi zai saki waccen sai ke kadai SUBHALLAHI!
Abin mamaki da takaici ga matan dake da wannan akida ta bin boka da ‘yan tsubbu domin mallakar miji shine zaka tarar dasu saboda imani da sukayi da aikinsu yana sa aji namiji har yaji in bake ba baya kallon kowace mace da kyau wato BIYAYYA.
Da yawan matan nan sun manta da wannan kalmar ta-kai ta kawo ma suna sawwara cewa ai su ya kamata yayi wa biyayyar don haka kowane irin abu zasu yi domin kai waga wannan matsayi.
Kaso mafi tsoka na matan da suka rage a kan wannan bakar al’ada matasane daga shekara 20 zuwa 40 sakamakon bakar hudubar data shige su kan cewa kaskanci ne namiji yayi miki kishiya alhalin baki wuce shekarun kuruciya ba tambaya gare su shin sun manta cewa ita kishiya da aure kaddarace wallahi in aka kaddara masa aure ko a dakin bori zaki kwana sai yayi.
Sannan ya kamata a ce mu gane cewa karin aure ga namiji hujjace kadan ne daga maza kan kara aure don ra’ayi amma da yawa bukatar halittarsu ke sanya kafin auren.
Yi biyayya ga miji domin samun tsira duk abinda ya baki umarnin kiyi toh kiyi shi matuk’ar be keta addinin musulunci ba, biyayya ga miji na k’arawa mace k’ima, martaba da mutunci,har ma da cigaba a rayuwa kuma yana k’ara soyayyarta cikin zuciyar mijin ta, sannan kuma zai kasance mai alfahari da ita koda kuwa baya yaba halinki na gari toh! A bayan idonki sai ya yaba miki kuma yasan me kike yi koda ace be tab’a furta miki ba.
Ba kowacce mace ce take iya jure yin biyayya ga mijinta ba, da yawan mata shaid’an yakan rinjayi zuk’atansu wajen sab’awa miji da kuma take umarnin sa wanda dalilin hakan mace takan jefa kanta halin data sani, tunda daman aljannar mace na k’ark’ashin tafin k’afar mijinta.
Kiyi biyayya ga miji domin samun tsira musamman a wannan wata da muke ciki na *Ramadan* in kikayi biyayya gare shi sai ki samu duk ladan da mata na gari suke samu koda ace kin saba sab’a masa dalilin faranta masa da yin biyayya da kika yi cikin wannan wata sai kiga ya yafe miki laifukan ki na baya ki had’a ladan ki gaba d’aya na cikin wannan wata mai alfarma mai albarka.