• Sat. Jun 22nd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Idan Safara’u Ta Amince Zan Aureta – Wani Matashi Ya Roki A Fada Mata Sakonsa

ByLucky Murakami

Aug 5, 2022

A yau munzo muku da jawabi tsohuwar jarumar masana’antar kannywood wanda ta haskaka a cikin shirin mai dogon zango na talabijin din arewa 24tv mai suna kwana casa’in safara’u.

Safara’u tayi suna cikin ƙanƙanen lokaci a cikin shirin kwana casa’in duba da irin yadda ta nuna halayenta kyawawa a cikin shirin amma kash anyi kusan zango ukku da ita sai ga bidiyon tsiraicin ta ya fita a kafafen sada zumunta wanda yayi sanadiyar anka fitar da ita daga shirin kwana casa’in.

Bakin nan kuma shikenan tauraronta bai sake haskakawa sai yanzu kuma munka samu labari wanda ya tabba ta koma mawakiya.

Safara’u ta fara waka tare da Mr 442 wanda yayi wakar tsiraicin Maryam booth wakar su ta farko ita “kwalelenku”.

A cikin wakar ta yi baiti wanda ya zamo shagube da habaici ga masana’antar kannywood inda take cewa :-

“Na chanza gida na chanza kala

Na bar sana’ar yan wahala.“

Abubuwan dai safara’u yanzu sai dai ace Allah ya shirya bawansa amma tayi nisa sosai.

Amma duk da haka kuma daman Hausawa kance so hana ganin laifi duk kallon lalacewar da ake gani da safara’u tayi ga wani ya fito ya nuna cewa zai aureta idan ta amince kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

“Ku fadawa Safara’u idan ta amince zan Aure ta, na amince!”

Wanda nan take wani daga cikin abokansa wanda hadimin dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Abban hajiya yayi alkawalin cewa:-

“Jama’a ku shaida.

Abokin mu SA Muhammad T. Shehu ya amince yana son Safarau. Indai ta amince ni nayi alkawarin zan bada sadakin auren.

Kuma na tabbatar mutane zasu basu gudunmawar data dace.

Malam Isah Abbas Ahmed, Muawiyya Alqali Inuwa ku shaida.”

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *