AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Home » Illolin Auren Mace Yar Jami’a A Wannan Zamani
    Education

    Illolin Auren Mace Yar Jami’a A Wannan Zamani

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiAugust 20, 2022No Comments4 Mins Read
    Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email
    Share
    Facebook Twitter LinkedIn WhatsApp Pinterest Email

    Yau zamu cikakken bayani akan wannan maga: Waɗanda su ke ƙyamar auren ƴar Jami’ah a daina ganin laifin su!

    Ai gudun mugun abu shi ya sa su ƙyamar.

    Ku kuma ƴan Jami’ah idan kuna so a daina ƙyamar auren ku to ku gyara kan ku mana.

    Ai ba wai ilimin ne naku ake ƙyama ba, hanyar da kuke bi ta neman sa ne ake ƙyama ta jefar da tarbiyyar da iyayen ku suka baku a gida da zarar kun je jam’ah ku kama hanyar watsewa da tanbaɗewa!

    Hakanan in ma kun samu ilimin maimakon ku yi amfani dashi ta hanyar data dace, sai ku koma yin fito-na-fito da dokokin da addinin ku ya shinfiɗa muku musamman ta fuskar aure, ba kwa bin dokokin Allah, ba kwa yin biyayya ga mazajen auren ku.

    Hasali ma komawa ku ke yi ku na ɗaukar cewa wai take muku haƙƙi ake yi ana bautar da ku kawai saboda mugun karatun Yahudu da Nasara da kuka koyo.

    KAR KU DAƊA, KAR KU RAGA, WAƊANNAN SU NE DALILAN DA KE SA AKE ƘYAMAR AUREN KU.

    AMMA IN DA ZA KU GYARA HANYAR NEMAN KARATUN NA KU, SANNAN KU YI AMFANI DA SHI TA HANYAR DA TA DACE, BA WAI ILIMIN NA KU YA ƊORA MUKU GIRMAN KAI DA YIWA DOKOKIN ALLAH TSAURIN IDO BA, ME ZAI SA AJI ƘYAMAR AUREN KU?

    AI NA TABBATA SAI KUNFI KASUWA MA, SABODA BABU WANDA BAYA SON YA AURI MAI ILIMI KODA KUWA SHI BAI DA SHI!

    Amma kuwa idan kika bi waccan hanya ta tanbaɗewa a jami’ah, wataƙila kin samu wani ɗan jami’ar ku ya hure miki kunne, yai miki ƙarya cewa zai aure ki idan kun gama karatu, ke kuma da yake sakarya ce baki da hankali kika yarda kika sakar masa jikin ki ya gama lalata ki, ba zai tashi nuna miki baki da tunani ba sai karatu yazo ƙarshe kiga yana ta ƙirƙiro abinda zaki rasa kan sa har sai yaga kun yi break up kun ɓata.

    Kokuma da zarar kun yi graduating ba ki kuma jin ɗuriyar sa, idan kin matsa da neman sa wataƙila ya yo miki text cewa bayan ya koma gida hajiyar su ta zaɓa masa mata kan dole ba yadda ya iya, kuma ƙarya yake yi kawai manufar sa itace tunda yasan cewa tareda shi kuka lalace a jami’ah, to fa ba zai auri lalatacciya ba, rayuwarki da shi ta jami’ah ce kawai ba zata kai ga aure ba daga nan sai ya barki da neman adduar ƴanuwa musulmi kan Allah ya kawo mijin aure layi yai miki nauyi.

    Haka zalika in ma kin kammala karatun ne aka yi sa’a ki kai auren, sannan kika ce ke ba zaki yi biyayyar aure yadda Allah ya umarce ki ba saboda kina taƙamar kinyi ilimin boko kinsan ƴancin ki, to ki sani har abada ba zaki taɓa samun jin daɗin aure ta sahihiyar hanya ba.

    Domin tarin irin wannan karatun baya mallakawa mace miji, bin dokokin Ubangiji kuwa, da yiwa miji biyayya su ke mallaka mata miji, su samar mata da cikar nutsuwa da kwanciyar hankali agidan ta na aure.

    Idan kuwa tace ba zata yi hakan ba to fa saidai tai wa mijin nata asiri ta dabaibaye shi kamar yadda ayau da yawan irin waɗannan matayen abinda suke yiwa mazajen su kenan, suka ɗauki hanyar shirka da tsafi suna mallake mazajen su, su ka bar hanyar Allah saboda wancan mummunan koyi da miƙa tunanin su da su ka yi ga miyagun Yahudawa har suka raba su da Allah suka ɗora su akan hanyar zuwa wuta.

    Dama Ubangiji ya faɗa mana cewa su kafirai sunyi burin inama ku (musulmai) kuma kun kafirce kamar yadda suka kafirce don ku zamo ɗaya da su.

    Shiyasa kullum su ke kan ƙoƙarin raba mu da Allah da koyarwar addinin mu.

    LALLAI NE MU YI TAKA TSATSAN DA SHARRIN SU DOMIN YA GAME KO’INA!

    Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email

    Related Posts

    Yobe State University, ABU collaborate on 12 months IJMB programm

    December 15, 2022

    Apply For Michael Taiwo Annual Scholarship for Graduate and Undergraduate Study

    December 13, 2022

    Why Schools Need Virtual Reality Technology Today

    October 7, 2022

    How Safe Is Your Data When Applying For An Online Payday Loan?

    October 7, 2022

    How to prepare well for the start of the school year?

    October 6, 2022

    Top 15 Universities In Nigerian In 2022

    October 6, 2022
    Add A Comment

    Leave A Reply Cancel Reply

    Check Also

    Ya Kamata Kusan Da Wadannan Tsaruka Na Tallafi Da Ake Bawa Yan Nigeria

    January 27, 2023

    FG Begins SMEDAN ₦1.5m Loan – Application Portal

    January 20, 2023

    How to Obtain an Ecowas ePassport as a Holder of a Nigerian Passport

    January 20, 2023

    Easy Way to Apply for a Visa in Nigeria

    January 20, 2023

    Apply 2023 Microfinance Bank Kaduna Recruitment

    January 20, 2023
    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2023 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.