Daga bakin mai ita shiri da bbchausa hausa take gabatarwa lokaci zuwa lokaci shirin shina za ana hira da mutane musamman mawaka da jaruman masana’antar Kannywood.
Yau anyi hira da jaruma Maryam Yahaya jarumar tayi kokari wajen amsa tambayoyin da ake mata saidai akwai tambayar da aka mata tace tana jin bakin ciki idan ta tuna zata mutu.
Fitacciyar jarumar Kannywood, Maryam Yahaya yayin zantawa da BBC Hausa ya shaida cewa babu abinda ya fi bakanta mata rai kamar ta tuna cewa watarana zata mutu ta tarar da Allah.
Idan ba a manta ba, a shekarar da ta gabata ne jarumar ta yi wani gagarumin ciwo wanda yasa ta fita daga hayyacin ta har wasu suka dinga tunanin mutuwa zata yi.
Ciwon ya yi matukar sauya mata halitta har ta kai ga wadanda suka san ta basa gane ta, yanzu haka dai ta warke sarai tamkar bata taba ciwo ba.
https://www.youtube.com/watch?v=WYendyLhLKU
A ranar Alhamis, 17 ga watan Maris a wani bidiyo wanda BBC Hausa ta wallafa na tattaunawar da aka yi da ita ta bayar da takaitaccen tarihin ta.
Ina matukar jin bakin ciki idan na tuna wataran zan mutu na koma wurin Ubangiji ~ Maryam Yahaya
Me za ku ce?
Wannan wasu kalamai ne da wata gidan jaridar suka bayyana cewa jarumar kannywood Maryam yahaya itace tayi wannan maganar.