• Thu. May 23rd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Ina Matan Suke: Muhimman Sirruka 7 Na Saka Jigida Da Kuma Amfaninsu

ByLucky Murakami

Mar 2, 2024
Amfanin saka jigida ga mata

A kokarin mu na kawo muku bayanai da labarai wanda zasu sa ku nishadi da kuma baku ilimi na zamantakewar rayuwa amihad.com ta kawo muku muhimman sirruka bakwai na saka jidigi ga mata.

Kamar yadda jaridar PremiumTimes ta rawaito Jigida wasu duwatsu kanana ne dake da nu’i daban daban da ake jera su a igiya ayi sarka da su ana sakawa a kwankwaso domin kwaliya.

Wannan irin kwaliyan ya fi suna a wurin matan yankin Nahiyar Afrika. Wasu kasashen har da maza ma sukan saka jigida.

Bisa ga al’adun gargajiya mutanen Afrika baya ga kwaliya akwai wasu dalilai da yasa suke saka jigida musamman matan su.

Sirruka da amfanin jigida ga mata guda 7

1. A wasu yankunan ana hada jigida mata su saka domin samun kariya daga iska ko mutanen boye, wato aljanu.

2. Wani jigidan akan haɗa da surkulle ne domin wai ya kare mace daga kamuwa da cututtuka musamman kananan yara.

3. Wasu jigidan akan haɗa su mace ta saka a kwankwaso domin samun saukin naƙuda a lokaci haihuwa.

4. Akwai yakinin cewa saka Jigida na taimakawa wajen rage kiba musamman ga mata masu tumbi ko katon ciki.

5. Jigida na taimakawa wa mace wajen ƙara girman kugu wato Hips a Turance, dakuma samun farin jini cikin mutane

6. Jigida na ɗaya daga cikin abubuwan dake jawo sha’awa da ra’ayin namiji zuwa ga mace.

7. Mafi rinjaye daga cikin maza suna son gani mace sanye da jigida domin ta zama abin jawo hankalinsu.

Sai dai kuma duk da wadannan kyawawan dalilan wasu mutane da dama basu son jigida saboda a ra’ayinsu jigida sarka ne da ake amfani da shi domin wani tsafi.

Wata mata da ta shahara a hada jigida Felicia Musa ta ce tana matukar sha’awar jigida musamman idan mace ta saka shi yana kara idan tana tafiya.

Ta ce jigida iri-iri ne akwai wanda wasu matan ke sakawa na farin jini ko na samun kariya amma yi hakan ba shine ke mai da mutum matsafi ba.

Felicia ta ce saka jigida ra’ayi ne idan kana so ka saka idan ba ka so ba za ka saka ba amma rashin son shi din ba shine zai ba mutum daman cusa wa mutane ra’ayin kin shi ko rashin son shi ba.

 

Kada Ka Furta Wadannan Kalaman A Gaban Mace A Farkon Haduwarku

Na kanga wasu mazan suna kuskuren furta wasu kalamai marasa daraja a farkon haduwarsu.

To a gaskiya kada ka sake ka rika furta irin wadannan kalaman domin zasu hanaka samun soyayyar wacce ka furtawa su.

Wadannan kalaman sune:

1. Tabbas ana iya shawo kan mace idan musu ya hadaku. Amma hakan na iya faruwa ne ba tare da kayi musun da ita bane domin neman soyayyar ta.

Idan Ka ja macen da kukayi haduwar farko kuma kake sonta da musu kana iya rasa soyayyar ta.

Duk wata mace Gimbiya ce, bita ta yadda take so cikin sauki zaka samu kanta.

Amma da zaran ka mata musu zata daukeka a namiji mai tsaurin hali hakan zai sa ta gujeka.

2. Kada ka sake ka aibata wani abu da ka gani a tare da ita koda kuwa shigar data yi ne. Kana hakan kuwa ka rasa ta.

Akwai mazan da suke nunawa mata iyaye da nuna musu shigar da suka yi ko kwalliyar su bai dace dasu ba a haduwarsu na farko. Kada kayi hakan.

3. Wasu mazan tsabar zakewa yana haduwa da mace a farko zai yi kokarin kai mata hannu ya taba mata jiki. Abokina mace ko cinikin jikinta take wasu na da zabi.

Bare kuma bakasan ko wacce iri bace har ka kai mata cafka a haduwarku na farko. Kuskure ne.

4. Mata sunada tsarguwa. Kada Ka sake kayi rada a gaban mace da kuka soma haduwa. Domin kawai zata dauka kayi mugun magana ne a kanta kamin kuma ka shawo kanta zai dau lokaci.

5. Kada ka kuskura aibata mata ko kushe wata a gaban macen da kukayi haduwar farko. Hakan zai sa ta samu shakku akan ka.

Da fatan maza musamman gayu da suke tunanin sun hadu zasu fahimta.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *