Yan mata da dama suna shiga cikin tarkon shedanun samari su yaudaresu suyi ta zina da su da tunanin zasu auresu saboda rashin sanin wasu taku na ma yaudarar maza.
Ga wasu daga cikin alamun da zaki yi sauri da saukin fahimtar saurayin ko namijin da yanzu haka kike soyayya dashi ba aurenki yakeson yi ba zina kawai yake son yi dake.
1: Zaki ga cewa bai yabon halayenki ko dabi’unki masu kyau kullum maganan halittun jikinki yafi magana maimakon wasu halayenki.
2: Bazai miki maganan aure ba kuma idan kin masa bai daukan zancen da mahimmanci.
3: Yana gudun ‘yan uwanki danashi su ganki. Don haka da wuya yagabatar dake a wajen wasu na kusa dake kuma zai rika kaucemiki idan kika bukaci yaga wasu naki nan ma zai rika zullewa.
4: Mafiyawan lokaci yafison ki ziyarceshi maimakon shi ya rika zuwa wajenda kika.
5: Yana son gayyatarki wuraren shakatawa da holewa maimakon wajen da zaki samu karuwa na addini ko na wani illimin zamani.
6: Wasu alamun shine idan kikayi wani kuskure baya iya fitowa a fili ya nuna miki saboda babu son gaskiya a zuciyarsa kada ranki.
7: A duk lokacin da kuka kadaita burinsa shine ya tabaki ko ya jawoki a jikinsa.
8: Sakonninsa na waya zantukan batsa da yabon halittarki sunfi yawa maimakon wasu maganganu da zai miki masu mahimmanci.
9: Duk hiran da zaku yi da wuya ya rika zuwa miki da zantunka da zai amfani rayuwanki. Ko hira yadda zai taimaki rayuwanki.
10: Bai damuwa da kokarin saninki, tarihin ki dana zuri’arku. Ko sanin abubuwan da kike burin yi ko zama.
Wadannan sune wasu daga cikin alamun da zaki iya fahimtar saurayin namiji mai sha’awan zina dake ba aure ba.
Da fatan idanuwaku zasu bude ku iya fahimtar masu sonku na gaskiya.
Thanks for the news line