Bayan yawan tambayoyi da korafe-korafe da mutane akan rabuwar auren Sani Danja da matarsa Mansura Isah an samu jin ta bakin ita matar inda ta fadi dalilan da zasu hana ta komawa kamar yadda binciken amihad.com ya tabbatar.
Jaridar Leadership Ayau ta rawaito cewa Mansurah Isah tsohowar matar fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Sani Musa Danja, ta bayyana cewar, tana matukar bukatar komawa dakin mijinta wato gidan Sani Danja a matsayin matarsa amma tana fargabar yin abun da zai kasance akwai sabon Allah a ciki.
Ta ke cewa, “Na fi ku son na koma gidan Sani Danja, amma idan zama ya haramta sai hakuri.”
Idan za ku iya tunawa Sani da Mansurah sun rabu a matsayin Ma’aurata ne a ranar 27 ga watan Mayun 2021 wanda mutuwar aurensu ya zama abun muhawara.
Jarumar wacce a karin farko take cewa dukkanin masu nemanta da ta koma gidan uban ‘ya’yanta tana jinsu kuma tana amsar shawarorin bi-hasalima ta fi su son komawa gidan na Danja amma in akwai haramci a ciki ta hakura duk yadda yake sonshi ko yake sonta.
Jaruma ta shaida wa majiyar DCL Hausa ta mujallar fim magazine cewa ta shelanta labarin rabuwar nasu ne domin kada jama’a suke ganin tana rayuwarta yadda take so su ga kamar tana wasa da aurenta.
Mansurah, wacce suka haifi ‘ya’ya hudu da Sani Danja (mace daya, maza uku), ta ce ko da farko ma abin da ya sa ta sanar da duniya labarin rabuwarsu, ta yi hakan ne domin kada a matsayin ta na fitacciya a gan ta da wani a waje ko ta tsaya da wani a rika yi mata kallon tana wasa da aurenta ko kuma ma a ce bata dauki auren da daraja ba.
To Allah ya kyauta 🤲