Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Entertainment

    Ina Tallan Pure Water Amma Maza Sun Dame Ni Da Karbar Lamabar Waya Akan Titi

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiJuly 17, 20223 Comments2 Mins Read

    The business of selling plastic water called ‘Pure Water’ and synthetic water ‘Bottled Water’ and other types of lemons on the streets has become common around the world due to the acceptance of the business as a way to get money. and kobo for those who do it and help those traveling in vehicles and even on the ground when the need arises

    Sana’ar sayar da ruwan leda da a ke kira da ‘Pure Water’ da ruwan roba ‘Bottled Water’ da nau’ikan lemuka a kan tituna ya zama ruwan dare gama duniya sakamakon karbuwa da sana’ar ta samu a matsayin hanyar samun taro da kobo ga masu yinta da kuma taimakawa masu zirga-zirga a ababen hawa da ma a kasa abin jika makoshi a lokacin da bukatar hakan ta kama.

    Wata zukekiyar budurwa mai sayar da ruwa a Accra babban birnin kasar Ghana ta koka kan yadda maza ke tsayar da ita amma ba don su sayi ruwa ko lemon da ta ke talla ba, a’a, sai kawai don su karbi lambar wayarta da nufin su kirata bayan ta gama tallan don su fahimci juna.

    Sai dai kuma wannan mai sai da ruwa ba wata bace illa fitacciyar mawakiyar kasar Ghana nan Nina Ricchie ta yi bad da kama a wani salo na yaki da munanan dabi’u a cikin al’umma, musamman ta’adar dora talla ga ‘yan mata

    Nina ta dora a shafinta na Instagram yadda ta sha fama da samari a dan fita da ta yi talla na dan sa’o’i kadan, inda ta yi kokarin bayyanawa iyaye irin hadarin da ‘ya’ya mata suke fuskanta a lokacin da suka fita talla.

    Sau tari ‘yan mata masu talla na karewa ne da tallata kansu a maimakon kayan da suka dauko talla

    Related Posts

    Uba Ya Hada Baki Da Abokinsa Sun Yiwa Yarsa Fyade

    November 26, 2022

    Kalli Bidiyon Sabuwar Rawar Da Safara’u Tayi Wanda Ta Jawo Mata Matsala Wajen Mutane

    November 24, 2022

    Kalli Abinda Mutane Suka Yiwa Hamisu Breaker Lokacin Da Ya Kaiwa Mahaifiyarsa Ziyara

    November 21, 2022

    Haryanzu Babu Namijin Da Yazo Mun Da Maganar Aure, Wata Jaruma Ta Koka Kan Rashin Mijin Aure

    November 17, 2022

    Bidiyon Yadda Amarya Taki Sumbatar Ango A Gaban Jama’a Saboda Yana Warin Baki

    November 17, 2022

    Kalli Abinda Jaruma Momee Gombe Da Wani Jarumi Sukayi A Gidan Gala Ko Kunya Babu

    November 15, 2022
    View 3 Comments

    3 Comments

    1. Pingback: Lamba ta maza ke amsa maimakon siyan kayan sana'a ta, Dirarriyar budurwa ta koka | Labarun Hausa

    2. Pingback: Budurwa tayi wuff da mahaifin tsohon saurayin ta, ta bada dalilan ta | Labarun Hausa

    3. Alamin on August 16, 2022 11:20 pm

      [email protected]

      Reply
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.