Yan kwanakin nan yan Kannywood sun matsa wajen nuna sha’awarsu da tsunduma cikin harkokin siyasa wanda har anga wasu daga cikinsu sun tsaya takara.
Jarumi Shu’aibu Lawan da aka fi sani da Kumurci ya ce yana da burika da dama a ransa, daga ciki akwai burinsa na son zama shugaban kasar Nijeriya duba da yadda ya ga lamurra na ta kara tabarbarewa.
Kumurci ya bayyana hakan a wata hira da BBC hausa suka yi da shi a cikin shirinsu mai suna daga bakin mai ita
“Hakika ina da burika masu yawa, cika hada burina na son ganin na zama shugaban kasar Nijeriya duba da yadda nake son na ga na gyara abubuwan da suka dagule a kasar” in ji shi.
‘Yan Kannywood Adam Abdullahi Adam wanda aka fi sani da Daddy Hikima ko kuma Abbale, da fitaccen mawaki, Aminu Ladan Abubakar da aka fi sani da Alan Waka, da kuma Naziru Dan Hajiya sun fito takara a kakar siyasar 2023 mai zuwa.
Duka su uku sun fito takara ne a karkashin jamiyyar ADP, wacce dan majalisar Birnin Kano da Kewaye, Sha’aban Ibrahim Sharada, yake yi wa takarar Gwamna a jihar Kano.
Allah yakyauta