Northern Habiscus ta bayar da labarin cewa “Na farko dai tana da shi ainahin uban yaran ta wanda sukayi auren saurayi da budurwa.
Se ta dan samu dan aikin contracts Haka ba a rasa ba a Abuja se take yawan zuwa se ALLAH ya hada ta da wani, da yai mata Fatin Aure se goganiya ta yarda.
Se take musu shift, na garin Su sati biyu na Abuja sati biyu. Duk a cikin Su ba wanda ya Sani.
Can Za tayi tafiya turai ta hadu da wani bayarabe shima yayi ta yin aure ta ce mishi ba matsala aka dada daurawa.
Yanzu igiya nawa? Tara kenan ko?
Shi kenan ana nan ana nan, se ta kara haduwa da wani yai mata ta yin Aure har an fara prep se 4th husband yace Bari ya dan bincika shine fa asirin oganiya ya Tonu.
Da ran 4 ya bacci duk se da ya sannar da mazajen hajiya!!! Abu dai beyi dadi ba.