Tun da lokacin maulidi ya karatota anji malamai sunata musayar yawu akan bikin maulidi kamar yadda wani malamain izalah yace yin kashi yafi Maulidi domin kuwa Annabi S.A.W ya koyar da yadda ake yin shi,amma fa Maulidi bai koyar ba haka kuma Sahabban sa basu koyar ba.
Hakan yasa malamai da dama ta kowane bangare suke maida zafafan marnain kamar yadda zamu kawo muku a kasa sai ku kuji ta bakinsu.
A bangeren darika wani malami yace duk da sa’in sa da ake yi a farko, tsakiya da ƙarshen wannan wata mai albarka, akan halarci ko akasin hakan na Maulidi, malamin ya ƙara da cewa kamata ya yi Musulmi su kasance masu girmama watan na Maulidi kasancewar a watan ne Allah S.W.A ya bai wa duniya kyautar da babu irinta watau samun haihuwar fiyayyen halitta Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Bugu da ƙari, babban malamin ya zayyano gamida lissafa wasu abubuwan da ya kamata a kasance masu gudanar wa a yayin Maulidi, inda yace:
Taro domin nuna mu’ujizar Annabi da halayensa domin yin koyi da shi.
- Yin azumi
- Sada zumunci
- Ziyartar marasa lafiya a asibiti
- Yin sadaKa
- Ciyar da jama’a
https://www.youtube.com/watch?v=oaZTMvnk2CU
Daga karshe malamin yaja hankali ga barin abubuwan da suka saɓawa shari’ar Muslunci ba, yayin gudanar da Maulidi, waɗannan abubuwa kamar yadda malamin ya bayyana sun haɗa da cakuɗuwar maza da mata, ihuce-ihuce, shaye-shaye da dai sauransu.