Wani abin tausayi da zai iya sanya hawaye ko kuka shi ne, cin karo da yarinyar da bai kamata a ce an ganta airin wannan wuri ba, wannan ya hada kankantar shekaru, da kuma yunkurin ganin sai kwatanta abin da na gaba dai ta ke yi, mafi muni shi ne, wadanda suke da halayya ta neman mata, ko kuma mazinata su ne ke ta kokarin ganin sun kusance ta.
Za ka ga mutum wanda a haife ya yi jika da ita, amma ba shi da burin da ya wuce ya ga kusance da kwanciya.
Wakilinmu ya ce ya taba ganin yarinyar da duka-duka shekarunta ba su haura 12 zuwa 23 ba wacca saboda kankantarta ma in ban da aiken ta ba a bin da ake iya yi, amma wasu kuma kullum bukatarsu su ga sun kawar da ita.
Ba wannan ne ya bani mamaki ba, yadda a wasu lokutan za ka ga tana rike da karan taba sigari a hannunta tana zuka, hakan na nuni da ita ma ta fara hawa kan turba kenan.
Wani babban abin tausayi da ya gani a mazowa gidan domin aiwatar da sana’arsu shi ne, ganin masu manyan shekaru daga sashen wasu mata da har yanzu basu san Annabi ya faku ba a gidan suna zuwa kallon yadda yara matasa ke cashewa madadin su tub asu koma ga Allah.
Wani abin da zai baka takaici kuma shi ne, Gidan Dirama ba gida ne da tsofaffin karuwai ke kwana ba, a a duk wacce ka gani in ma dai budurwa ce ta baro gidan iyayenta, ko kuma a a bazawara ce mai kuruciya da idan ba ta gaya maka ba ba za ka san sirrinta.
A halin yanzu mafi aksarinsu ba suna baro gida ne domin za a yi musu auren dole kamar a da can ba, a a suna fita ne domin sun fi karfin iyayensu su fada musu su ji, wasu ma suna fita ne da izinin iyayen domin su iyayen sun san ko da sun fada ba za su ji ba.
Wakilimmu ya samu zantawa da wata uwar ‘ya’ya uku ‘yan mata biyu da namiji daya da ta nemi a sakaya sunanta, wadda daya daga cikin ‘ya’yan nata ta fita zuwa irin wannan gida na Dirama, inda ta bayyana masa cewa, ita ce ta bar yarinyar zuwa wannan gida.
“Gaskiya ni ce nake barinta ta je don kai na, dalili kuwa shi ne, gara dai ko me za ta yi nasan tana dawo wa gida ai zan san halin da take ciki fiye da a ce ta fita ina fushi da ita, kuma ta ki dawowa gida.
“Ka san yaron yanzu ka haife shi ne amma ba ka haifi halinsa ba, ai ina nan zaune take kawo min labarin wasu suna shafe shekara da shekaru ba su dawo gida ba. Ita dai ‘yar uwarta ka ga tana zuwa makaranta ta addini da ta Boko amma dai ita waccan mu nan muna ta addu’a Allah ya shirya mana, na yi kuka a farkon lamarin har na hakura sai dai‘yar uwarta ta ce ba ni hakuri, amma dai ban taba yi mata baki ba,”in ji ta.
To ko yaya ‘yan uwan irin wadannan‘yan mata ke ji a ransu yayin da aka ce ‘yar uwarsu ta shiga irin wannan yanayi? Aminu wa ne ga ita wannan yarinya, ya bayyana wa wakilimmu irin halin da ya tsinci kansa lokacin da ya shigo ya samu mahaifiyarsu na kuka.
“Hankalina ya yi matukar tashi da na shigo gida na samu ummanmu tana kuka, abin da ban saba gani ba, da na tambayi daya kanwar tamu ta fada min abin da yake faruwa, na ji kamar raina zai fita, ana cikin haka sai ga ta ta shigo,babarmu ba ta taba hana ni abu na ki ba amma a ranar da fara dukanta ban ma san tana cewa na bari ba, kuma daga ranar har yanzu ba na yi mata Magana idan ta zo gida,” in ji shi.