Wani matashi dan kasa da shekaru 20 ya hallaka mahaifinsa kan sabani da suka samu a tsakaninsu a gona.
Yaron ya yi wa tsohon kisan gilla ne saboda dattijojin ya yi masa tambaya a gonar a ranar Juma’a da yamma a kauyen Issele-Uku da ke Karamar Hukumar Aniocha, Jihar Delta.
Wani ganau a kauyen ya ce, “Matashin ya kashe mahaifinsa ne bayan dattijon ya bi shi gona yana tambayar dalilin da ya girbe masa amfanin gona ba da izininsa ba.
“Tambayar da tsohon ya yi masa a gonar kan dalilin girbe masa amfanin gona ba da izini ba ne ya fusata matashin ya kashe shi.
“Yaron ya yi kokarin tserewa, amma mutanen kauyen Ukpati suka ritsa suka damka shi ga ’yan sanda.
“A jawabinsa a hannun ’yan sanda ya bayyana nadamarsa bisa abin da ya aikata.”
A cewarsa, wanda ake zargin ya ce, “Shi ya same ne a gona ina aiki, yana kokarin kwace addar saboda ba ma shiri da shi.
“Da ya dauki adda yana kokarin ya sare ni, shi ne na sa ita ce na tare shi, sannan na buga masa itacen.
“A lokacin da zai fadi, wayar ta fadi kasa, san na dauke ta, ba san cewa mutuwa zai yi ba.
“Da itace na yi amfani, kuma kowa ya gani, babu komai a hannuna lokacin da na tafi gona.
“Itace na buga masa sau uku, ban san cewa abin da na yi zai yi ajalin mahaifina ba.”
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Delta, DSP Edafe Bright, ya ce, “tabbas an yi haka.”