• Sun. Nov 10th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Iyayen Dalibai Ku Taimaka Ku Roki ASUU Ta Janye Yakin Aiki – Sakon Gwamnatin Tarayya

ByLucky Murakami

Aug 5, 2022

Labarin da muke samu daga shafin BBCHausa shine gwamnatin Najeriya ta nemi iyayen ɗalibai a ƙasar da su roƙi malaman jami’a su jingine yajin aikin da suke yi tsawon wata biyar “saboda ta yi abin da za ta iya”.

Ƙaramin Ministan Ƙwadago Festus Keyamo ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyana ta cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels a yammacin Juma’a.

Ministan ya ce tun kafin ƙungiyar malaman ta ASUU ta fara yajin aikin gwamnati ta kira su don tattaunawa amma duk da haka sai da suka tafi yajin aikin.

Da aka tambaye shi ko me zai faɗa wa iyayen da yaransu ke ci gaba da zaman gida har yanzu, sai ya ce: “Zan ce musu su je su roƙe su [ASUU]. Kamar yadda shugaban ƙasa ya faɗa a baya, waɗanda suka san su su roƙe su don nuna kishinsu ga ƙasar.”

Ya ci gaba da cewa: “…Me za mu yi fiye da haka? Tun kafin a fara yajin aikin muka kira su. Ba wai ƙyale su muka yi ba kawai muka kama barci. Ba zai yiwu ka ƙyale mutum ya ci kwalarka ba kuma ya tilasta maka ciyo bashin naira tiriliyan ɗaya.”

A farkon makon nan ne ASUU ta sake tsawaita yajin aikin da take yi da mako huɗu, ƙari a kan wata biyar da ta shafe bayan jingine aiki a jami’o’in Najeriya.

Sai dai kuma da dama mutane basuji dadin wannnan magana da gwamnatin tarayya tayi ba inda suke fara maida martani kamar haka:

Idris Najib yace:

“Don Allah Kuji Lalacewa, Uwar Kudin Da Buhari Yake Ciyowa Bashi Suna Ina, Mai Yasa Gwamnati Buhari Ta Rewa Mu Yan Nigeria Dan Allah,”

Aisha Abubakar Imam tace:

“A roki gomnati ta debo musu kudi daga cikin wanda AG ya diba, a hau teburin sulhu ku koma bakin aiki.”

Maryam Shanono tace:

“Sunfi kowa sanin abinda zasuyi Asuu ta daina yajin aiki ai shine wani sabon rainin hankali zasu ce wai iyayen yara su rokesu toh ya batun hakkokinsu kuma after iyayen yaran sunyi rokon.”

Hafiz Nura yace:

“Indai sai na roƙi ASUU sannan yaro na zai koma makaranta to an daɗe ba a daina karatun boko a Nigeria ba! Allah ya yi wadaran wannan gwamnatin ta Buhari da APC.”

Jaafar Nahuta yace:

“Zan so gaskiya ayi hira dani a BBC ko kuma wani kafofin labarai Wanda zai bani dama in fada wasu ra’ayuyyuka na da kuma Allah wadai da wannan gwamnati.”

Kadan daga cikin ra’ayoyin mutane kenan akan wannan lamarin. Me zakuce ta naku bangaren?

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *