Labarin da muka tattaro daga jaridar Premium Times ya kawo cewa Jihohi takwas sun yi mirsisi sun ƙi biyan ma’aikatan su albashin aƙalla watanni shida. Wani rahoto ne ya tabbatar da haka.
Jihohin sun haɗa da Taraba, Edo, Ebonyi, Ondo, Filato, Imo, da Abiya. Rahoton ya ce sun ƙi biyan ma’aikata albashin kuma sun kasa biyan ‘yan fansho haƙƙoƙin su.
Kungiyar BudgIT ce ta fitar da rahoton inda ta ce aƙalla jihohi 12 a cikin jihohin Najeriya 36 ba su biya aƙalla albashin wata ɗaya ko sama da haka ba ya zuwa 28 Ga Yuli, 2022.
Jihar Abiya ba ta biya wasu daga cikin ma’aikatan jihar albashi ba tsawon watanni 22.
“Jihar Abiya ta kasa biyan albashin ma’aikatan manyan makarantun gaba da sakandare tsawon watanni shida, yayin da Jihar Ebonyi ba ta biya haƙƙin ‘yan fansho na tsawon watanni shida ba.” Inji BudgIT.
Rahoton ya nuna ma’aikatan sakateriyar Jihar Taraba sun koka kan yadda ake masu tsallaken watanni wajen biyan albashin aƙalla tsawon watanni shida. Su kuma malamai a manyan makarantun jihar Ondo da jami’an unguwar zoma na asibitin jihar Ondo ba a biya su albashin watanni huɗu ba.
Wani ma’aikatacin gwamnatin Jihar Ondo ya shaida wa wakilin mu cewa su na cikin wani mawuyacin hali. “Ana biyan mu albashi a baya. Amma rabon da a biya mu tun cikin watan Fabrairu, 2022. Daga watan Maris zuwa yanzu ko sisi ba a biya mu ba.” Inji ma’aikaciyar.
Sai dai Kwamishinan Ilmin Jihar Ondo, Bamidele Olateju, ya ce daga watan Afrilu ne ba a sake biya ba zuwa yanzu.
“An riƙa biyan albashi har zuwa watan Afrilu. Amma daga nan ne ba a sake biya ba. Amma muna bakin ƙoƙarin an biya na sauran watannin da su ka rage.” Haka ya shaida wa wakilin mu a ranar Juma’a.
Jaridar ta Premium Times ta tuntuɓi jihohin da su ka ƙi ko su ka kasa biyan albashin ma’aikatan su.
Jihohi takwas sun riƙe wa ma’aikata aƙalla albashin watanni shida.
Jihohi takwas sun yi mirsisi sun ƙi biyan ma’aikatan su albashin aƙalla watanni shida. Wani rahoto ne ya tabbatar da haka.
Jihohin sun haɗa da Taraba, Edo, Ebonyi, Ondo, Filato, Imo, da Abiya. Rahoton ya ce sun ƙi biyan ma’aikata albashin kuma sun kasa biyan ‘yan fansho haƙƙoƙin su.
Kungiyar BudgIT ce ta fitar da rahoton inda ta ce aƙalla jihohi 12 a cikin jihohin Najeriya 36 ba su biya aƙalla albashin wata ɗaya ko sama da haka ba ya zuwa 28 Ga Yuli, 2022.
Jihar Abiya ba ta biya wasu daga cikin ma’aikatan jihar albashi ba tsawon watanni 22.
“Jihar Abiya ta kasa biyan albashin ma’aikatan manyan makarantun gaba da sakandare tsawon watanni shida, yayin da Jihar Ebonyi ba ta biya haƙƙin ‘yan fansho na tsawon watanni shida ba.” Inji BudgIT.
Rahoton ya nuna ma’aikatan sakateriyar Jihar Taraba sun koka kan yadda ake masu tsallaken watanni wajen biyan albashin aƙalla tsawon watanni shida. Su kuma malamai a manyan makarantun jihar Ondo da jami’an unguwar zoma na asibitin jihar Ondo ba a biya su albashin watanni huɗu ba.
Wani ma’aikatacin gwamnatin Jihar Ondo ya shaida wa wakilin mu cewa su na cikin wani mawuyacin hali. “Ana biyan mu albashi a baya. Amma rabon da a biya mu tun cikin watan Fabrairu, 2022. Daga watan Maris zuwa yanzu ko sisi ba a biya mu ba.” Inji ma’aikaciyar.
Sai dai Kwamishinan Ilmin Jihar Ondo, Bamidele Olateju, ya ce daga watan Afrilu ne ba a sake biya ba zuwa yanzu.
“An riƙa biyan albashi har zuwa watan Afrilu. Amma daga nan ne ba a sake biya ba. Amma muna bakin ƙoƙarin an biya na sauran watannin da su ka rage.” Haka ya shaida wa wakilin mu a ranar Juma’a.
Kazalika jaridar ta tuntuɓi jihohin da su ka ƙi ko su ka kasa biyan albashin ma’aikatan su.
Wannan matsala ta zama ruwan dare a jihohi da dama, har ta sa wasu ma’aikatan yanzu sun fantsama yin wasu ƙananan sana’o’in rufa wa kai da iyali asiri.
Yayin da ɗawainiyar ciyar da iyali ta sha kan su, wasu sun koma ƙananan kasuwanci, haya da baburan okada, tuƙin taksi ko dillancin kayayyaki musamman mata a cikin gidaje da kasuwanni.
Haka kuma da yawa sun kama kiwon dabbobi, kiwon kifi da kiwon kaji.