• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Kalli Abinda Mr 442 Da Yan Matansa Safara’u Da Malika Sukayi A Wajen Wasan Su Na Garin Maiduguri

ByLucky Murakami

Oct 3, 2022

Wa’yannan mawakan a yanzu haka suna chan kasar Maiduguri domin gudanar da wani wasa na murnar zagayowar ranar da aka bawa Nigeria yancin kai wanda ake gudanarwa a kowanne state a kasar nan domin nuna farin ciki.

Wannan Magana idan kuka kalleta haka take babu wa’yanda ake zagi a wannan garin kamar wa’yannan mawakan amma kuma abinda zai baku mamaki shine a duk lokacin da sukaje waje sai aga ana shaukin zuwansu wanda akeyi musu wani abu domin nuna farin ciki wanda ba kowanne mawaki akeyi ba a wannan kasa ta Nigeria.

Mr442 shine wanda ya jagoranci tawagarsa zuwa wannan garin saboda suyi wasa kuma su nuna farin cikinsu suma akan wannan rana inda wannan wajen ya cika tam da mutane mata da maza duka a yayin wannan wasan wanda an yaba masa da nishadantar da mutane ta hanyar yi show.

Anga safara’u da sweet Malika duka a wannan wajen wanda sune ma suka karawa wannan wasan armashi ta hanyar yi rawa da kuma wasu wakoki wanda masoyansu suke so daga cikin wakokinsu.

https://www.youtube.com/watch?v=aOp6vanGjGU

Yan Maiduguri sunji dadi sosai daman suna daga cikin wa’yanda suke sun wannan mawakin saboda kowa yasan jihar Borno tana daga cikin manyan jihohi a wannan kasa shi yasa wannan mawakin baya daukar lokaci baije wannan garin ba.

Ganin wannan taron da yadda mutane suka cika a wajen taron haka ya daga hankalin yan uwansu mawaka domin sun gani a zahiri kullum kara yawan masoya sune me makon suna raguwa amma kuma sai yado suke meke faruwa ne inji yan kannywood.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *