KinyuwaBudurwar Da Ta Balaga Aure Da Huri Kalli Irin Hatsarin Da Zai Biyo Baya.
Idan muka kalli yanda kullum tarbiyyar society ɗin mu ke ƙara sukurkucewa duk da yanda wa’azi da nasiha da jan-hankali ya zama gidan kowa da akwai, tun daga cikin masallatai na khamsu salawati, gidajen Radio, social media, kasuwanni, wayoyin hannu da dai sauran hanyoyi da malamai ke isar da nasihohin. Sai nake ganin da zamu koma mu gwada furmular da Manzon Allah ya bayar kan tarbiyyar yara, da tayiwu (Astaghfirullah yaƙini gareni) mu samu mafita a nan.
Wato ina nufin ta hanyar komawa da kuma yin aiki da hadisin nan da duk wanda ya kai shekaruna, da na sama dani muka koya a islamiyyoyi, wanda daga baya ban san me ya faru ba yayi ɓatan dabo a makarantun islamiyyoyin.
Ina nufin hadisin nan da Manzon Allah (S) yake cewa “addibuu auladakum” ku ladabtar da ‘ya’yayanku, “ala thalathi khisalin” a bisa abubuwa uku, “hubbi nabiyyikum” SON ANNABINKU “wa hubbi ahali baitihi” DA SON IYALAN GIDANSHI, “wa ƙira’atil Qur’ani” DA KARATUN AL’ƘUR’ANI
Domin ita fa soyayya ta gaske, tana haɗe ne da biyayya, matuƙar yara suka sha soyayyar Shugaba (S) da iyalan gidansa, to tabbas zasu taso da kwaikwayon ayyukansu.
Maimakon muhimmantar da musabaƙa da ƙaƙale wajen karatun Alkur’ani (wanda shi ma wannan ɗin yana da kyau a mataki na uku kamar yanda ya zo a hadisin), to muke fara gabatarwa da yara ‘yan makaranta sanin ma’anonin ayoyin da suka zo kan yiwa Manzon Allah soyayya ta gaske kamar ayoyin:
1- لِتُؤْمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَتُعَزِّرُوهُ وَتُوَقِّرُوهُ وَتُسَبِّحُوهُ بُكْرَةً وَأَصِيلًا
Domin ku yi imani da Allah da ManzonSa, kuma ku ƙarfafe Shi, kuma ku girmama Shi, kuma ku tsarkake Shi safiya da maraice.
Kamar ayar
2- قُلْ إِنْ كَانَ آبَاؤُكُمْ وَأَبْنَاؤُكُمْ وَإِخْوَانُكُمْ وَأَزْوَاجُكُمْ وَعَشِيرَتُكُمْ وَأَمْوَالٌ اقْتَرَفْتُمُوهَا وَتِجَارَةٌ تَخْشَوْنَ كَسَادَهَا وَمَسَاكِنُ تَرْضَوْنَهَا أَحَبَّ إِلَيْكُمْ مِنَ اللَّهِ وَرَسُولِهِ وَجِهَادٍ فِي سَبِيلِهِ فَتَرَبَّصُوا حَتَّىٰ يَأْتِيَ اللَّهُ بِأَمْرِهِ ۗ وَاللَّهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفَاسِقِينَ
Ka ce: “Idan ubanninku da ɗiyanku da ´yan´uwanku da matanku da danginku da dukiyoyinku, waɗanda kuka yi tsiwirwirinsu, da fatauci wanda kuke tsoron tasgaronsa, da gidaje waɗanda kuke yarda da su, sun kasance mafiya soyuwa a gare ku daga Allah da ManzonSa, da yin jihdi ga hanyarSa, to, ku yi jira har Allah Ya zo da umurninSa! (Azabarsa), Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane fasiƙai.”
HAKANAN a muhimmantar da koyawa yara sanin daraja, ƙima da soyayyar ahali baitin Annabi, domin cikin soyayyarsu akwai soyayyar Annabi, ita kuma soyayyar Annabi na kaiwa ga masa ɗa’a, yiwa Annabi ɗa’a kuwa na kaiwa zuwa ga abinda Allah ya kira ‘abinda ke rayamu’ لما يحييكم
Kamar misali a ke sanarda su ma’anar ayar
…… قُلْ لَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْرًا إِلَّا الْمَوَدَّةَ فِي الْقُرْبَىٰ
…. Ka ce: “Ba ni tambayar ku wani lada a kansa, face soyayya ga makusantana”
Sannan a koyar dasu karatun AlƘur’ani tare da nuna musu irin treasure da mu’ujizar dake hannunsu, a muhimmantar da koyar dasu sanin ma’anonin Ƙur’ani da tuntuntuni a cikin ayoyinsa sama da mayarda shi wani kayan yin gasa, a koyar da su ayoyin dake magana kan taƙwa, rahamaniyyar Allah, bin dokokin Allah, da kuma garaɓasar dake cikin bin tsarin Allah a duniya da lahira.
To da tabbas a tunani na, da ɗan ƙaramin hangena, zamu shawo kan wannan lalacewar tarbiyyar da kaso mai yawa.
ALLAH YA LAƊAFA MANA YA GYARA MUNANAN AYYUKANMU.