AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Home » Kalli Annobar Da Tura Yan Mata Aikatau Ta Haifar
    Education

    Kalli Annobar Da Tura Yan Mata Aikatau Ta Haifar

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiSeptember 11, 2022Updated:October 4, 2022No Comments3 Mins Read
    Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email
    Share
    Facebook Twitter LinkedIn WhatsApp Pinterest Email

    A wani rubutu da jaridar Leadership Hausa tayi ta fadi kadan daga cikin matsalolin dake addabar mata musamman yara, matasa, ita ce tura su aikatau wassu garuruwa ba tare da la’akarin wadanne irin matsaloli za su fuskanta a can ba.

     

    Majiyar amihad.com ta rawaito cewa iyaye kan tura yara mata wasu garuruwa da sunan neman kudi ko samo abin duniya, wanda kafin a samu yaro namiji daya da aka tura aikatau sai an samu yara mata sama da goma da aka tura, me ya sa?

    Yana da kyau iyaye mata su fahimci cewar ‘ya mace abar tattali ce da kulawa, tana bukatar tallafi fiye da namiji ta kowacce fuska amma iyaye ba sa duba haka.

    Wasu iyaye dai bukatarsu a sama musu kudi ta kowacce hanya.

    Me ya sa iyaye ke tauye rayuwar ‘ya mace? Me ya sa ba za a ba ta dama ba ta yadda za ta kula da rayuwarta da na yaran da za ta haifa a gaba ba? Inda a ce za a ba wa yara dama a ji ta ra’ayinsu fiye da rabinsu ba wai suna so ba ne ake tura su wannan aikatau din.

    Matsalolin Da Tura Yara Mata Aikatau Ke Haifarwa Akwai matsaloli da tura yara mata aikatau ke haifarwa masu tarin yawa amma ga kadan daga cikin su:

    1: Yana hana ta neman ilmi.

    2: Yana dakushe mata mafarkinta ya hana mata cikar burinta.

    3: Yana bata tarbiyya.

    4: Yana mayar da ita marar ‘yanci.

    5: Yana mayar da ita tamkar baiwa

    6: Yana haifar da rashin tausayi a zuciyarta. Ta yadda za ta sa a ranta cewar ba a sonta ya sa aka kai ta wani wuri da sunan aiki wannan dalili sai ya kangarar mata da zuciya.

    7: Yana jefa yara harkar sace -sace.

    8: Wasu na fadawa harkar zinace-zinace.

    9: Karshe wasu su dawo gida da ciki hade da ciwon zamani.

    Ina Mafita?

    Mafita a nan ita ce:

    1: Iyaye mu sani cewar duk kudin da za a yi nema ta wani gari to ana iya samunsa a gida.

    2: Mu tabbata in zamu tura yara aikatau a yi yarjejeniyar ba su damar neman ilmi.

    3: A rinka bibiyar halin da suke ciki a kodayaushe.

    4: Mu saurare su a lokacin da muka kai musu ziyara ta nan za mu fahimci matsalarsu.

    5: Mu rinka tuntubar su ta wayar hannu mu ji labarinsu.

    6: Idan sun zo ganin gida mu tabbatar da mun bincike su.

    7: Mu sa ido sosai don ganin halayyarsu ba ta canja ba.

    8: Idan da hali mu kyale su su yi aikin kusa da mu muna ganin shiga da fitar su.

    Shawara

    A shawarce yana da kyau iyaye mu sa ni cewar babu alheri wurin tura yara aikatau wasu garuruwa, yara mata da yawa kan fada garari da kuncin rayuwa a lokacin da suka bar gaban iyayensu da sunan neman kudi a wurare dabandabam. Mu sani daraja da mutunci hade da rayuwar yaranmu sun fi mana komai a rayuwa. Iyaye mata a kula da wannan.

    Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email

    Related Posts

    Yobe State University, ABU collaborate on 12 months IJMB programm

    December 15, 2022

    Apply For Michael Taiwo Annual Scholarship for Graduate and Undergraduate Study

    December 13, 2022

    Why Schools Need Virtual Reality Technology Today

    October 7, 2022

    How Safe Is Your Data When Applying For An Online Payday Loan?

    October 7, 2022

    How to prepare well for the start of the school year?

    October 6, 2022

    Top 15 Universities In Nigerian In 2022

    October 6, 2022
    Add A Comment

    Leave A Reply Cancel Reply

    Check Also

    Ya Kamata Kusan Da Wadannan Tsaruka Na Tallafi Da Ake Bawa Yan Nigeria

    January 27, 2023

    FG Begins SMEDAN ₦1.5m Loan – Application Portal

    January 20, 2023

    How to Obtain an Ecowas ePassport as a Holder of a Nigerian Passport

    January 20, 2023

    Easy Way to Apply for a Visa in Nigeria

    January 20, 2023

    Apply 2023 Microfinance Bank Kaduna Recruitment

    January 20, 2023
    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2023 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.