• Sat. Oct 12th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Kalli Bidiyon Maryam Yahaya Ta Shawu Tayi Mankas

ByLucky Murakami

Aug 26, 2022

Cikin binciken da muka saba yi dan kawo muku labari wanda zasu kayatar daku, a yau munyi karo da wani bidiyo da mutane suke ta magana duba da irin abubuwan da jaruma Maryam Yahaya tayi a cikin bidiyon.

Kamar yadda shafin Hausamini ya rawaito wani bidiyon Maryam Yahaya ta shawu, inda ya jawo cece ku ce a shafukan sada zumunta, anga jaruma Maryam Yahaya tare da wasu maza biyu a wani bidiyo ta nuna yanayin kamar ta shawu tayi mankas.

Tun ba yanzun ba, dama anama jarumar zargin kamar tana shaye shaye, inda tun kwanakin baya aka ganta a wani bidiyon makamancin wannan, inda tayi mankas, wanda shima yaita yawo a kafafen sada zumunta.

Bidiyon dai yaci gaba da jawo cece ku ce, inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa akan bidiyon. Mun kawo muku bidiyon domin ku gani kuma, yadda jarumar tayi.

 

Inamatuqar Son Sake Komawa Gidan Tsohon Mijina Sani Danja Inji Tsohuwar Matarshi Mansurah Isah

Awata Fira Da Akayi Da Tsohuwar Jarumar Shirya Finafinan Hausa Ta Kannywood Waro Jaruma Mansura Isah Ta Bayyanawa Manema Labarai Cewar

“Na fi ku son na koma gidan Sani Danja, amma idan zama ya haramta sai hakuri”- Mansura

Tun bayan fitar labarin rabuwar aurenta da Sani Danja a ranar 27 ga Mayun 2021, a karon farko Jaruma Mansura Isah ta magantu inda ta ce jama’a da ke ta bata shawara kan ta koma gidan uban ‘ya’yanta ba su fita son hakan ba.

Jaruma ta shaida wa majiyar DCL Hausa ta mujallar fim magazine cewa idan zama ya haramta dole a yi hakuri da juna duk da yadda ake son juna.

Mansurah, wadda suka haifi ‘ya’ya huɗu da Sani Danja (mace ɗaya, maza uku), ta ce ko da farko ma abin da ya sa ta sanar da duniya labarin rabuwarsu, ta yi hakan ne domin kada a matsayin ta na fitacciya a gan ta da wani a waje ko ta tsaya da wani a riƙa yi mata kallon tana wasa da aurenta ko kuma ma a ce bata dauki auren da daraja ba.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *