Daukakin Malamai Sunyi Allah Wadai, Tare Da Kira Ga Hukuma Domin Su Dauki Mataki Kan Wannan Wakar Dama Ire Iren Wadannan Wakokin.
Sai Dai, Ado Gwanja Yace Shi Baiga Wani Abu Ba A Sabuwar Wakar Tashi Ta “CHASS” Inda Yace Shi Neman Abincinsa Yakeyi. Bawai Yayita Ne Saboda Wani Fitsara Ko Wani Hanyar Lalacewa. Kamar Yadda Mutane Ke Zato Kan Wakar.
Har Yanzun Mata Sunata Kokarin Hawa Sabuwar Wakar Ta Gwanja, Inda Suke Hawa Suna Raye Raye Na Rashin AlbarKa. A Shafukan Sada Zumunta.
Duk macen da take bin wakar Ado Gwanja CHASS ya kamata ta sani bata yiwa iyayen ta adalci ba kuma bata kyautawa ya’yan da zata haifa ba idan tayi aure idan kuma mai aurece bata kyautawa jikokin da yayan ta zasu haifa ba
Duniya dai makarantace lahira wajen hisabi anan zata ga sakamakon da ta aikata me kyau ko mara kyau kuma lahira gida 2 ne Aljannah ko Wuta wa’iyazubillah.
Annabi S.A.W ya bamu labari Lokacin da ya leka wuta sai ya ga mafiya yawa a cikinta mata ne ya Subhanallah yar uwa yi kokari ki kubutar da kanki daga shiga wuta.