Kamar yadda rahoton ya tabbtar mana shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙafur a Jihar Katsina, ya tabbatar da cewa fiye da gonaki 300 ne ƙanƙara ta fatattaka amfanin gonar da ke ciki a yankin sa.
Garba Kanya ya ce ibtila’in ya faru a gonakin da ke yankunan ƙauyuka takwas a cikin mazaɓu huɗu da su ka haɗa da Dutsen Kura, Kanya da
Gozaki.
Amfanin gonar da ya ce an tafka asara sun haɗa da masara, gero, shinkafa, waken soya, barkono waɗanda ya ce an yi asarar na miliyoyin nairori.
Garba ya bayyana haka lokacin da ya ke tattaunawa a ranar Litinin a Katsina.
“Ƙauyukan da lamarin ya shafa sun haɗa da Gidan Sabo, Kalabawa, Unguwar Tsamiya, Ɗandabo, Unguwar Wanzamai, Unguwar Ɗanwada, Unguwar Maigarma da Unguwar Fulani.
Ya ce ya ga abin takaici sosai a lokacin da ya kewaya yankunan da abin ya shafa, tare da Hakimin Ƙafur, Abdulrahman Rabe.
Sun yi wa waɗanda su ka yi asarar miliyoyin kuɗaɗe jaje, kuma ya ce su yi taw akkali tare da rungumar ƙaddara.
Ya ce sun sanar da Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA).