• Thu. Sep 12th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Kalli Yadda Jaruman Kannywood Suka Gudanar Da Bikin Maulidin Annabi

ByLucky Murakami

Oct 12, 2022

Irin wannan abin suke sai kullum suke shiga zukatan al’umma saboda agarin Kano matukar mutum zai nuna tsantsar soyayya ga Annabi to babu shakka zaiga yadda jama’a suke bibiyarsa suke nuna masa shima so kamar yadda yake son Annabi.

Duk Hassadar mutum yasan kwarai da gaske yan kannywood suna son Annabi domin duk wani abu da ake na Annabi zakaga su aciki koda Acikin tiktok ana yawan ganin jarumai da dama suna hawa wakokin yabon Annabi wannan shine yasa akayi musu shaidar suna kaunar Annabi.

A yayin da wannan watan ya kama wanda a shine aka haifi shugaban mu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama dan haka ake gabatar da wani taro wanda za’aci asha domin nuna farin ciki ga samuwar Annabi.

Sai dai suma yan kannywood ba’a barsu abaya ba inda suma suke nuna nasu farin cikin kamar yadda sauran jama’a suke wanda wasu sukan taru su ci su sha wasu kuma sukanyi wakoki na yabo duka domin farin ciki da wanan watan kowa da irin yadda yake nuna nasa farin ciki.

https://youtu.be/JcelKkj-utg

Hakika yan kannywood sun dauko salon da dole su shiga zukatan al’umma saboda Annabi shine karshe yafi komai daraja a wajen Allah matukar kanson Annabi to Allah zai soka.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *