• Thu. Mar 28th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Kalli Yadda Wani Mai Adaidaita Sahu Ya Saka Talabijin A Ciki Dan Debewa Kwastoma Kewa

ByLucky Murakami

Sep 8, 2022

Kamar yadda muka samu labari wani saurayi, Muhammad Al Amin, ya kawata babur din da yake sana’arsa ta haya da talabajin da kuma wurin cajin waya a Kano.

Muhammad ya yiwa babur dinsa mai kafa uku kwaskwarima, inda ya makala talabijin na bango kirar Plasma a ciki, ta yadda idan ana tafiya fasinja za su rika yin kallo domin debe kewa kamar yadda zaku gani a bidiyon dake kasa.

A hirarsa da Aminiya, Al Amin ya kara da cewa, “Na sa kayan cajin waya daban-daban har guda goma sha daya, yadda zai kasance duk irin wayar da ka zo da ita za ka iya sa caji, kuma ko ku nawa ne.” Jaridar Aminiya ta rawaito.

A cewarsa, sakamakon kwaskwarimar da ya yiwa babur din nasa, ya samu alheri mai yawa daga mutanen da ke zuwa su hau daga ciki da kuma wajen Kano.

Sannan bai kara ko kwabo ba a farashin da ake daukar mutane zuwa ko’ina ba a cikin garin Kano.

Ya bayyana cewa da farko ya sa talabijin din ne domin amfanin kansa, saboda a duk lokacin da aka dauke shi shata, idan suka je wani wuri aka ajiye shi yana jira, sai ya kunna ya rika yin kallo.

Amma daga baya sai hakan ya burge jama’a, har suna sha’awar hawa babur din nasa, suna tafiya, suna kallon talbijin har su je inda za su sauka.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

One thought on “Kalli Yadda Wani Mai Adaidaita Sahu Ya Saka Talabijin A Ciki Dan Debewa Kwastoma Kewa”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *