Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Family & Relationships

    Karshen Abun Kunya: An Kama Amarya Tayi Sata Lokacin Aurenta

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiAugust 29, 2022No Comments2 Mins Read

    Labarin da muke samu shine ’Yan sanda sun kama amarya kan laifin sata a wajen bikinta kamar yadda majiyaru ta tabbtar.

    Jaridar Aminiya ta rawito cewa hukumomin ’yan sandan kasar Uganda suna tuhumar wasu jami’ansu hudu da laifin kama wata amarya a wajen biki inda suke zarginta da laifin sata.

    Kakakin rundunar, Mista Fred Enanga, ya ce ana tuhumar ’yan sandan da yin abin da bai dace ba, lamarin da ake ganin zai sa su iya rasa aikinsu.

    ’Yan sandan sun kama amaryar ce ana tsakiyar bikinta a ranar Asabar da daddare inda suka kai ta ofishinsu da ke garin Mbararata, a yammacin kasar Uganda ta kuma shafe daren a tsare sai washegari da safe aka sake ta.

    Rundunar ’Yan sandan kasar ta ce jami’an nasu sun kama amaryar ce ba tare da kwakkwarar hujja ba.

    Mista Enanga ya ce lamarin sam bai yi dadi ba, domin ga amaryar ranar farin cikinta ya zame mata ranar bakin ciki.

    Dan sandan ya ce yanzu haka an kama daya daga cikin ’yan sandan da suka aikata wannan rashin kirki, sauran ukun kuma sun buya inda ake neman su ruwa a jallo.

    Shugaban wurin da amaryar ta yi aiki a baya ne ya zarge ta da sata, shi ya sa ya fada wa ’yan sandan hudu su kuma suka dira wajen bikin tare da yin awon gaba da ita.

    Related Posts

    Yadda Kanin Miji Ya Dirkawa Amaryar Yayansa Ciki A Nasarawa

    November 19, 2022

    Sati Biyu Kacal Da Yin Aure Amarya Ta Bukaci Ango Ya Saketa Saboda Baya Iya Gamsar Da Ita A Kan Gado

    November 18, 2022

    Yadda Ake Kwalliyar Maida Tsohuwa Yarinya

    November 7, 2022

    Lokuta Da Yawa Maza Yan Iska Sunfi Iya Soyayya Wata Budurwa Ta Kira Ruwa

    November 5, 2022

    Yadda Ango Yayi Dawowar Bazata Ya Kama Matarsa Da Babban Abokinsa Suna Cin Amanarsa

    November 4, 2022

    Bidiyon Hira Da Matar Da Take Auren Maza Biyu Kuma Suke Kwana Kan Gado Daya

    November 3, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.