Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    News

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiDecember 12, 2022No Comments2 Mins Read

    Richard Nana Sam, dan kasar Ghana ne wanda ransa yayi matukar baci, sanadiyyar wani lamari dake wakana a gidan shi, wanda ya yanke shawarar fallasa wa a kafafan sada zumuntar zamani, da sa ran samun mafita.

    Yayin bada labarin kalubalen da yake fuskanta a wata sananniyar kungiyar ‘yan Ghana dake da shafi a Facebook, ya kwashe labarin tun daga farko har karshe. Legit na ruwaito

    Richard ya bayyana yadda yayi wa yaran shi tagwaye (namiji da mace) masu shekaru 19 hayar malamar da za ta dunga koya musu karatu a gida.

    Malamar ta ce, tana dauke da ciki wata uku
    Kamar yadda Richard ya fadi, ya tabbatar da bai zabi malami namiji ba, saboda ba zai iya kasadar dawowa gida wata rana yaji labari mara dadi tsakanin mai koya karatun da diyarsa ba.

    Amma ga mamakin sa, malamar mai shekaru 28 tazo wurin shi wata rana, ta na shaida mishi labarin abunda yayi kokarin guje mawa.

    “Masoya na, bayan wata takwas da ta dauka tana koyar da yara na, wata rana malamar ta zo ta shaida mun tana dauke da cikin yaro na wata uku, inda shi yaron nawa ya amince da lallai cikin nashi ne.

    “Ta ce, ta na kaunar yaro na, saboda haka tana so in yarje musu su yi aure,” a cewar Richard.

    Martanin jama’a
    Tsokacin yan soshiyal midiya:

    “Theodora Mawuse Norvor cewa yayi:”Wani lokaci mika lamarin yaran kake ga Ubangijin da ya baka su. A matsayin ka na dan adam, duk iya son da kake wa yaron ka, kuma ka ke son kare su, ba za ka iya ba, Ubangiji kawai zai iya.”
    Nana Ama Darkowaa ya nuna:

    “Mafitar a nan shi ne amincewa da cikin, kula da bukatun matar har ta haihu. Sannan ka gamsar da yaron ka cewa, ba zai iya aure a shekarun shi ba, a halin yanzu dole ya maida hankali a kan karatun shi, sai yayi aure daga baya idan ya mallaki hankalin kan shi, koda da malamar shi ce.”
    Kabeiku Quansah ya bayyana cewa:

    “Ina rokon ka da kada ka bari su yi aure fa! Waye ya ce soyayya ne kadai matakin aure. Ka bar yaron ka ya cigaba da neman ilimin shi, alabashshi ka cigaba da kula da cikin, tunda ya amince da nashi ne.”

    Related Posts

    Tofah Bayan Ganin Bidiyon Tinubu Yana Motsa Jiki, Malmai Sun Fara Zazzago Martani

    January 11, 2024

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022

    Yadda Aka Kama Malamin Addini Yana Lalata Da Yan Mata Biyu Yan Uwan Juna

    November 23, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.