• Sat. Oct 12th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Ko Fir’auna Iyakaci Irin Wannan Rashin Tausayi Na Buhari – Sheikh Bello Yabo

ByLucky Murakami

Jul 25, 2022

Kamar yadda da yawan mutanen sun kalli bidiyon yadda masu garkuwa da mutanen jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna watannin baya da suka wuce, wanda cikin bidiyon anga yadda masu garkuwa da mutanen suke azabtar da mutanen harda dukansu da bulala.

Da yawa daga cikin mutanen suna cikin mawuyacin hali na neman taimako cikin gaggawa kafin wani abu marar dadi yazo ya faru dasu.

Sako cikin bidiyo daga bakin Babban Malamin Musulunci Sheikh Bello Yabo Sokoto, yace Buhari wannan rashin tausayin naka ko kaine Fir’auna iyakar abinda zaka iya yi kenan, abin yayi yawa.

Bayan Sheikh Bello Yabo mutane da dama musamman a shafukan sada zumunta da gidajen rediyo da talabijin sunata Allah wadai da wannan al’amari.

[ads1]

Tabbas ana aikata kowani irin nau’in zalunci da ta’addanci a wannan Kasa tamu Nigeria karkashin jagorancin Baba Buhari Maigaskiya, abinda kawai ya rage shine Buhari yayi da’awar Allantaka kamar yadda Fir’auna yayi, ba ma fatan haka ya kasance da shugaba Buhari.

Ga bidiyon martanin da Sheikh Bello Yayi akan wannan abu daya faru.

Ba abinda ya kama illar muci gaba da addu’ar Allah ya kubutar da wadannan mutanen daga hannunsu.

 

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *