• Sat. Jul 20th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Ku Daina Aikata Wadannan Abubuwan Da Zarar Kunyi Aure

ByLucky Murakami

Mar 5, 2024

Aure yana kara daukaka darajan namiji Musamman idan ya kauce aikata wasu munanan abubuwan da yake aikatawa kamin yayi aure.

Ga wasu abubuwan da ya kamata duk namiji ya daina yinsu bayan yayi aure

1. Da zaran kayi aure, kayi kokarin rage mu’amalar ka da matan da bakada wata alaka na dole dasu

Yawan ci gaba da mu’amala da tarin mata a matsayin kawaye hanya ce kawai na zubda mutunci matar da kake aure dama kanka.

2. Ka guji yiwa wasu matan karya na yaudaran aure bayan kayi aure

Wasu mazan sukan ci gaba da rainawa matan da suka yaudara hankali na cewa duk da wannan auren da sukayi zasu auresu. Muddin har kayi aure, kada ka yi wasa da zuciyar wata macen dakasan ba auren ta nan gaba da gaske zaka yi ba.

3. Da zaran kayi aure ka kauracewa yin hiran tsakar dare a waya da wasu matan.

Babu wani da ya zamemaka dole sai kayi hira da shi ko ita a tsakar dare bayan ga matarka a tare da kai.

[ads1]

4. Akwai wasu kyautuka na musamman da masoya suke baiwa junansu bayan sunyi aure su rika amfani dasu irin zobe.

Duk abunda kasan matarka ta baka kada ka sake ka cire shi.

5. Dole ne ka koyi shawara da matarka.

Shawara irin na abunda ya shafi gida, ciki da haihuwa dole ne kayi da matarka. Haka manyan al’amura na rayuwarka yanada kyau ka tattauna da ita domin fahimtar da ita ko neman shawaranta.

6. Ga mazan da suka saba da yawon dare dole ne su daina da zaran sunyi aure.

Zuwa gidajen rawa ko zuwa gidajen karuwai ba na mai mata bane. Don haka da zaran kayi aure da guje musu.

7. Daga lokacin da kayi aure, daga wannan lokacin girma ya zo maka.

Don haka dabi’a na shaye shaye dole ne ka ajiye su a gefe domin fuskantan rayuwa mai tsafta.

[ads1]

8. Zaman majalisa da maza suke yi ba na magidancin kwarai ba.

Idan ma kana yi kamin kayi aure, ka tabbatar da cewa ka daina da zaran an shafa fatiha.

9. Kada ka sake kayi wasa da hanyoyin da aka dauraka na neman kudi.

Wasu mazan kamin suyi aure basu sanin nauyin da yake kan mai aure na yin hidma. Wannan yasa suke wasa da samunsu. Da zaran kayi aure, kada ka sake kayi wasa da neman kudi da zaran kayi aure

10. Duk da zina kamin aure haram ne. Zina bayan aure yafi muni matuka.

Ka kaucewa kula matan banza bayan kayi aure.

Da fatan maza sabbin aure zasu ki yaye wadannan abubuwan domin mutuncin kansu dana iyalansu.

To jama’a kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *