Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    News

    Kuskure Ne Rufe Titi Lokacin Sallar Juma’a Inji Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiJuly 23, 2022No Comments1 Min Read

    Babban Malamin addinin musulunci a Najeriya kuma Khalifan Kadiriyya na Afirka ya caccaki masallatan juma’an da suke rufe hanya a yayin sallar juma’a da cewa kuskure ne wanda Annabi Sallallahu Alaihi Wa sallam ya yi hani da shi.

    A yayin karatun littafin hadisi na “Attajul Jami’u Lil’usul Fi Ahaadisir Rasul” da yake gudana a kowanne mako shehin Malamin ya karanto hadisin da ya yi hani da yin salla a wurare bakwai wanda cikinsu har da tsakiyar hanya.

    “Ba adalci ba ne rufe hanya a yayin sallar juma’a da wasu masallatai ke yi.

    [ads1]

    Akwai masu lalura, akwai mara lafiya ko mace mai haihuwa, ko wanda suka yi hadari da za a kai asibiti wanda rufe hanyar ke sanya su cikin mummunan yanayi.

    Ya kamata ko me za a yi kar a rufe hanya baki daya a dinga rage hanya ko yaya take.

    Wani shi ma limami ne zai je ya ba da sallar juma’a mutane na jiransa, amma an tare masa hanya.
    Wannan ba adalcin musulunci ba ne.” A cewar Khalifan Kadiriyya Shaikh Qaribullahi Amirul Ansar.

    Related Posts

    Tofah Bayan Ganin Bidiyon Tinubu Yana Motsa Jiki, Malmai Sun Fara Zazzago Martani

    January 11, 2024

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    December 12, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.